Coronavirus: Babu wajen gwaji a yankuna 4 cikin 6 na kasar nan

Coronavirus: Babu wajen gwaji a yankuna 4 cikin 6 na kasar nan

A yayin da cutar Covid-19 ke ci gaba da kamari a duniya kuma ana ci gaba da samun masu cutar a Najeriya, har yanzu babu wajen gwajin cutar a yankuna hudu cikin shida na kasar nan.

An gano cewa babu kayan gwajin cutar a yankunan Kudu maso gabas, Arewa maso yamma, Arewa maso gabas da kuma Arewa ta tsakiya duk kuwa da cewa ana ci gaba da tsoron yaduuwar cutar a cikin miliyoyin jama’ar da ke jihohin 19 na yankunan.

A dukkan kasar Najeriya, dakuna gwaje-gwaje biyar ne suke da kayan aikin gwajin cutar kuma suna nan ne a yankunan Kudu maso yamma da Kudu-kudu.

An gano cewa akwai manyan dakunan gwaje-gwaje na gwamnatin tarayya guda biyu a jihohin Legas da kuma Osun.

Dayan dakin gwajin kuwa yana jihar Edo yayin da daya yake birnin tarayya Abuja, wanda dukkan Arewa da kuma Kudu maso gabas suka dogara dashi.

Dakunan gwajin da aka gano sun hada da na NCDC da ke Abuja, dakin gwaji na asibitin kwararru da ke jihar Edo, dakin gwaji na asibitin koyarwa na jihar Legas, cibiyar binciken Najeriya da kuma cibiyar kula da cutuka ta jihar Osun.

Coronavirus: Babu wajen gwaji a yankuna 4 cikin 6 na kasar nan
Coronavirus: Babu wajen gwaji a yankuna 4 cikin 6 na kasar nan
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Dattijuwa 'yar shekara 103 da ta kamu da Coronavirus ta warke (Hoto)

Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa a halin yanzu cibiyoyin nan biyar kan cika da mutane masu son gwajin cutar koda kuwa basu bayyana da wata alamarta.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa, dakin gwaji daya ne da gwamnatin jihar Legas ta mallaka wanda yake asibitin da ake killace masu cutar. Jami’an kuwa sun tabbatar da cewa mutane na ta tururuwar zuwa duba lafiyarsu a kyauta.

“Ina tsoron zuwan cutar nan Arewa ya zama babbar matsala saboda babu wajen gwajin cutar. Koda kuwa za a gwada, sai an dauka mai cutar zuwa nesa,” Nafiu Yusuf, mazaunin garin Dutsin-Ma da ke jihar Katisna yace.

Wani likita da ke aiki a asibitin Malam Aminu Kano ya yi kira ga gwamnonin yankin Arewa da kada su jira gwamnatin tarayya. “Su hana taron jama’a kuma su rufe makarantu. Su kuma dage wajen samar da kayan amfanin gaggawa. Duk da muna addu’ar cewa kwayar cutar ba za ta iso kusa damu ba,”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel