Hatsari ba sai a mota ba: Rijiya ta kashe mutane 2, ta jikkata jami’in kwana-kwana

Hatsari ba sai a mota ba: Rijiya ta kashe mutane 2, ta jikkata jami’in kwana-kwana

Masu iya magana su kan ce wai ‘Hatsari ba sai a mota ba’ wasu mutane biyu sun gamu da ajalinsu sakamakon tsautsayi da ya shigar dasu cikin wata tsohuwar rijiya a kauyen K-Vom dake cikin karamar hukumar Jos ta kudu a jahar Filato.

Punch ta ruwaito mutanen biyu sun gamu da hatsarin ne a lokacin da suke aiki a cikin rijiyar, inda suka zurma cikin wani kogo dake cikin rijiyar, daga nan jama’an yankin suka kira Yansanda, wanda su kuma suka kira jami’an hukumar kwana kwana don bayar da agaji.

KU KARANTA: Annobar Corona: Jerin Jahohi 13 a Najeriya da suka rufe makarantu tare da hana taron jama’a

Sai dai a kokarin wani jami’in hukumar kwana kwana na ceto mutanen ta hanyar janyo su waje, shi kansa da kyar ya tsallake rijiya da baya, amma duk da haka sai da ya samu rauni babba a kan sa, inji majiyar Legit.ng.

Shugaban hukumar kwana-kwana ta jahar Filato, Mista Samuel Nzwak ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace: “Abinda ya faru shi ne wasu Yansanda sun shiga ofishinmu a Bukuru da safe suka nemi mu kai ma wasu mutane biyu dauki da suka fada cikin rijiya a K-Vom.

“Koda muka je mun tarar da mutanen sun mutu, amma sai muka yi kokarin fiddosu daga rijiyar, a lokacin da jami’anmu suka shiga cikin rijiyar da nufin fiddo mutanen ne sai kwatsam wani dutse da bamu san inda ya fito bay a fada a kan jami’in mu dake cikin rijiyar.

“Ya samu mummunar rauni a kansa, amma dai mun gaggauta mika shi zuwa asibiti, kuma daga rahoton da na samu shi ne yana samun sauki, gaskiya mun yi bakin cikin aukuwar lamarin.” Inji shi.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jahar Kaduna ta sanar da yi ma wasu gungun yan bindiga kisan gilla, tare da kubutar da mutane biyu da suka yi garkuwa dasu a kauyen Daku, karamar hukumar Giwa ta jahar Kaduna.

Mataimakin kwamishinan Yansandan jahar Kaduna, Onah Sunny ne ya bayyana haka a Kaduna inda yace: “Bayan an sanar da Yansanda, sai muka tura jami’an suka tare yan bindigan kafin su kai sansaninsu, a nan muka yi bata kashi dasu, muka kashe dan bindiga daya, sa’nnan muka ceto Dauda da dan uwansa.

“Sai dai dan uwan nasa yana asibiti yana samun kulawa, da yake jami’anmu sun nuna ma yan bindigan fin karfi, ala dole suka tsere, suka jefar da baburansu guda shida. Haka zalika mun kwace bindigu 2 kirar AK-47, alburusai, wayoyin salula kirar Techno, fitila, layu da kudi N268,000.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Jos
Online view pixel