Coronavirus: An hana masu gidajen haya karbar kudin haya a Uganda da Kenya

Coronavirus: An hana masu gidajen haya karbar kudin haya a Uganda da Kenya

- Biyo bayan barkewar cutar coronavirus a nahiyar Afirka, gwamnatocin kasashen Kenya da Uganda sun umarci masu gidajen haya da su daina karbar kudin haya

- Wannan na kunshe ne a wassu takardu mabanbanta da shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni da kuma wani likita daga Kenya a ranar 18 ga watan Maris na 2020

- Rahotanni sun tabbatar da cewa za a kwace kadarar duk wanda ya take dokar ko kuma ya zauna a gidan yari na shekaru 70 ko kuma a fuskanci dukkan hukunci

Biyo bayan barkewar cutar coronavirus a nahiyar Afirka, gwamnatocin kasashen Kenya da Uganda sun umarci masu gidan haya maza da mata da su daina karbar kudin hayan ‘yan haya na kwanaki 90 a kasashen.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, wannan na kunshe ne a wassu takardu mabanbanta da shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni da kuma wani likita daga Kenya a ranar 18 ga watan Maris na 2020.

Rahotanni sun tabbatar da cewa za a kwace kadarar duk wanda ya take dokar ko kuma ya zauna a gidan yari na shekaru 70 ko kuma a fuskanci dukkan hukunci.

DUBA WANNAN: Dattijuwa 'yar shekara 103 da ta kamu da Coronavirus ta warke (Hoto)

A wata labari na daban, Wata mata mai shekaru 103 da haihuwa 'yar kasar Iran da ta kamu da cutar Coronavirus ta warke a ranar Laraba 18 ga watan Maris na 2020.

Duk da cewa mafi yawancin alkalluma na nuna cewa mutane masu shekaru da yawa ba su cika warkewa idan sun kamu da cutar ba, matar mai shekaru 103 da aka kwantar na kimanin sati daya a asibitin birnin Semnan ta warke kamar yadda kafar yadda labarai ta IRNA ta ruwaito.

An ruwaito cewa shugaban sashin binciken kimiyyan Lafiya na jami'ar Semnan Navid Danayi yana cewa, "an sallame ta bayan ya warke"

A cewar rahotonni ita mutum na biyu cikin masu yawan shekaru da ya warke, dayan wani mutum ne mai shekaru 91 a kudu maso gabashin Iran a cewar kafar yadda labaran Cibiyar Lafiya ta Duniya, WHO, ta yi kiyasin cewa cutar na kashe kimanin kashi 3.4 cikin 100 na wadanda suka kamu da ita.

Coronavirus: An hana masu gidajen haya karbar kudin haya a Uganda da Kenya

Coronavirus: An hana masu gidajen haya karbar kudin haya a Uganda da Kenya
Source: Twitter

Coronavirus: An hana masu gidajen haya karbar kudin haya a Uganda da Kenya

Coronavirus: An hana masu gidajen haya karbar kudin haya a Uganda da Kenya
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel