Annobar Corona: Hukumar INEC ta fasa gudanar da zabuka a jahohi 3
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta dakatar da gudanar da zaben cike gurbin da ta shirya gudanarwa a jahohin Bayelsa, Imo da Filato sakamakon bullar cutar Coronavirus.
Jaridar TheCable ta ruwaito mai magana da yawun hukumar, Festus Okoye ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis, 19 ga watan Maris, inda yace mazabun da suka shirya gudanar da zabukan sun hada da Bayelsa ta tsakiya da Bayelsa ta yamma.
KU KARANTA: Annobar Corona: Jerin Jahohi 13 a Najeriya da suka rufe makarantu tare da hana taron jama’a
Wadannan mazabu biyu na jahar Bayelsa su ne kujerun da sabon gwamnan jahar Bayelsa Diri Douye da mataimakinsa Lawrence Ewhrudjakpo suka sauka bayan sun samu nasara a zaben gwamnan jahar.
Sai kuma kujerar Sanatan mazabar Imo ta Arewa, wanda wakilin mazabar a majalisar dattawa,Sanata Benjamin Uwajumogu ya bari sakamakon mutuwarsa, sai kuma kujerar Sanatan mazabar Filato ta kudu, wanda Sanata Longjan ya bari bayan mutuwarsa.
“Sashi na 26 na kundin dokokin hukumar zabe na shekarar 2010 ya baiwa INEC daman dage zabe a sakamakon annoba ko bala’i, don haka ya zama wajibi hukumar ta dauki wannan mataki saboda zabe ya kunshi tara jama’a da dama a waje daya ne.
“Musamman tun daga gudanar da zabukan fidda gwani, tarukan masu ruwa da tsaki, horas da jami’an zabe na wucin gadi, da dai sauran ayyukan zabe, don haka duk da sanin da hukumar take da shin a hakkin yan Najeriya na samun wakilci a majalisa, amma bukatar kare lafiyan jama’a ta shafe wannan.” Inji shi.
Daga karshe yace nanbada jimawa ba INEC za ta sanar da sabbin ranakun da za’a gudanar da zaben, amma fa sai an samu nasarar dakile yaduwar cutar Coronavirus.
A wani labarin kuma, fadar shugaban kasa ta mayar da martani ga majalisar dattawa biyo bayan neman da ta yi na shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito ya yi ma yan Najeriya jawabi game da annobar cutar Coronavirus tare da kokarin da gwamnatinsa take yi ko hankulan jama’a zai kwanta.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya bayyana kiran da majalisar ta yi a matsayin kokarin bata ma shugaban kasa suna da kuma siyasantar da maganan, inda yace ya kamata yan majalisar su sani cewa yanzu ba lokacin neman suna bane.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng