Duk da tsoron coronavirus, za a yi sallar Juma'a a masallacin kasa na Abuja

Duk da tsoron coronavirus, za a yi sallar Juma'a a masallacin kasa na Abuja

- A jiya Alhamis ne majalisar koli ta kula da lamurran addinin Musulunci a Najeriya (NCSIA) ta bayyana cewa za a yi jam’in sallar Juma’a a babban Masallacin kasa da ke Abuja

- Mataimakin babban sakataren majalisar, Farfesa Salisu Shehu ya ce za a ci gaba da sauran al’amuran da suka shafi gudanarwa amma za a iya gyara shirye-shiryen

- Ya kara da kira ga Musulmai da su yi biyayya ga dokokin gwamnati don kariya da hana yaduwar cutar, wadanda suka hada da hana taro kowanne iri har da na addini

A jiya ne majalisar koli ta kula da lamurran addinin Musulunci a Najeriya (NCSIA) ta bayyana cewa za a yi jam’in sallar Juma’a a babban Masallacin kasa da ke Abuja.

Mataimakin babban sakataren majalisar, Farfesa Salisu Shehu, ya sanar da manema labarai a sakateriyar NSCIA din, cewa za a ci gaba da sauran al’amuran da suka shafi gudanarwa amma za a iya gyara shirye-shiryen.

Kamar yadda yace kuma jaridar Daily Trust ta ruwaito, da yadda al’amura ke tafiya a kasar nan, ana tsammanin gwamnatin za ta dau manyan matakai kuma matukar aka gindaya su, za su yi biyayya.

Duk da tsoron coronavirus, za a yi sallar Juma'a a masallacin kasa na Abuja

Duk da tsoron coronavirus, za a yi sallar Juma'a a masallacin kasa na Abuja
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Buhari ya karba bakuncin shugaban majalisar dattijai da gwamnan jihar Yobe (Hotuna)

Ba zamu tirsasa duk wadanda suka dakatar da yin sallar Juma’a ba, amma a babban masallacin kasa, zamu dau matakai ne saboda muna duban yadda lamarin ke tafiya,” yace.

Ya kara da kiran jama’a da su yi sallarsu ta farilla a gida sakamakon yaduwar muguwar cutar Covid-19.

Ya kara da kira ga Musulmai da su yi biyayya ga dokokin gwamnati don kariya da hana yaduwar cutar, wadanda suka hada da hana taro kowanne iri har da na addini.

“Abin alhini ne idan aka ce matsalar cutar coronavirus na daya daga cikin tashin hankalin da duniya ta ke fuskanta a wannan lokacin. Akwai bukatar kada a siyasantar da lamurran. Annabi Muhammad ya bada koyarwa ta sunna yadda zamu yi idan annoba ta barke kamar wannan a duniya,” yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel