Ganduje ya bayar da umurnin rufe dukkan makarantun Kano saboda Coronavirus

Ganduje ya bayar da umurnin rufe dukkan makarantun Kano saboda Coronavirus

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bayar da umurnin rufe dukkan makarantun gwamnati da na kudi a jiharsa a matsayin mataki na kare yaduwar annobar cutar Coronavirus da ke yi wa al'umma barazana.

Sanarwar mai dauke da saka hannun kwamishinan ilimi na jihar, Muhammad Sanusi Sa'idu Kiru ta bayyana cewa za a rufe makarantun ne daga ranar Litinin 23 ga watan Maris na shekarar 2020.

Sanarwar ta ce iyaye su tabbatar da cewa sun kwashe 'ya'yansu daga makarantun kwana kafin ranar Lahadi.

Ganduje ya bayar da umurnin rufe dukkan makarantun Kano saboda Coronavirus

Ganduje ya bayar da umurnin rufe dukkan makarantun Kano saboda Coronavirus
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Ganduje ya kalubalanci hukuncin kotu a kan binciken Sanusi II

Kamar yadda sanarwar ta ce, an dauki matakin ne domin kare dalibai da malamansu daga hatsarin kamuwa da cutar mai muni na Coronavirus da ta zama ruwan dare a duniya.

Sanarwar ta kara da cewa, "Ba an rufe makarantun bane domin a tayar da hankulan mutane sai dai domin a dauki matakin kariya bisa barazanar cutar da ke yaduwa a kasashen duniya."

Har ila yau, sanarwar ta kuma shawarci iyaye su tabattar 'ya'yansu na kula da tsafta a yayin da suke zaune a gida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel