Dattijuwa 'yar shekara 103 da ta kamu da Coronavirus ta warke (Hoto)

Dattijuwa 'yar shekara 103 da ta kamu da Coronavirus ta warke (Hoto)

Wata mata mai shekaru 103 da haihuwa 'yar kasar Iran da ta kamu da cutar Coronavirus ta warke a ranar Laraba 18 ga watan Maris na 2020.

Duk da cewa mafi yawancin alkalluma na nuna cewa mutane masu shekaru da yawa ba su cika warkewa idan sun kamu da cutar ba, matar mai shekaru 103 da aka kwantar na kimanin sati daya a asibitin birnin Semnan ta warke kamar yadda kafar yadda labarai ta IRNA ta ruwaito.

An ruwaito cewa shugaban sashin binciken kimiyyan Lafiya na jami'ar Semnan Navid Danayi yana cewa, "an sallame ta bayan ya warke"

A cewar rahotonni ita mutum na biyu cikin masu yawan shekaru da ya warke, dayan wani mutum ne mai shekaru 91 a kudu maso gabashin Iran a cewar kafar yadda labaran

Cibiyar Lafiya ta Duniya, WHO, ta yi kiyasin cewa cutar na kashe kimanin kashi 3.4 cikin 100 na wadanda suka kamu da ita.

Dattijuwa 'yar shekara 103 da ta kamu da Coronavirus ta warke

Dattijuwa 'yar shekara 103 da ta kamu da Coronavirus ta warke
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Ganduje ya kalubalanci hukuncin kotu a kan binciken Sanusi II

Amma ga mutanen da shekarun su ya haura 80, wadanda ke mutuwa sun kai kashi 21.9 cikin 100 a cewar wani rahoton na WHO da ta gudanar tare da gwamnatin China.

A wani rahaton kun ji cewa kungiyar kiristoci ta Najeriya, CAN, ta umarci mabiyanta da su dakatar da duk lamurran bauta da zai tara jama’a a waje daya.

Kamar yadda gidan talabijin din Channels ya ruwaito, kungiyar addinin ta bada sanarwar nan ne don a shawo kan yaduwar cutar a kasar nan.

Rabaren Joseph Hayab, shugaban kungiyar na jihar, wanda ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar, ya shawarci cocina da su rage ibadu ko kuma su gajarce lokacin ibadun idan ya zama dole ayi shi.

Hayab ya kara da bayyana wasu matakan kare kai daga cutar don mabiyan su kiyaye tare da gujewa samun cutar.

Babban faston ya kara jaddada umarnin cewa dole ne a taimaka wajen kare yaduwar cutar don haka a karanta shan hannu da rungumar juna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel