COVID-19: Daliban da ke kasar China suna lafiya kalau - Gwamnatin Jigawa

COVID-19: Daliban da ke kasar China suna lafiya kalau - Gwamnatin Jigawa

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce dukkan dalibanta da ke karatu a Jamhuriyar China suna nan lafiyan su kalau duk da bullar anobar Coronavirus a wasu sassan kasar da kasashen duniya.

Gwamnatin jihar ta ce daliban suna cigaba da daukan darussa ta yanar gizo yayin da suka kebe kansu a gidajensu domin kare kansu daga kamuwa da kwayar cutar kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Sakataren dindindin na ma'aikatan lafiya na jihar, Salisu Mu'azu ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da suka kira a Dutse babban birnin jihar.

COVID-19: Daliban da ke kasar China suna lafiya kalau - Gwamnatin Jigawa
COVID-19: Daliban da ke kasar China suna lafiya kalau - Gwamnatin Jigawa
Asali: Depositphotos

A cewarsa, jihar a shirye ta ke idan an samu bullar annobar domin tuni an ware wurin kebe mutane an kuma kafa kwamiti ta musamman domin kulawa da annbar idan ta bulla a jihar.

DUBA WANNAN: Ganduje ya kalubalanci hukuncin kotu a kan binciken Sanusi II

Wannan sanarwar ta Mu'azu tana zuwa ne a yayin da wasu iyayen daliban da gwamnatin jihar ta dauki nauyin karatunsu a kasar ta China ke nuna damuwa game da lafiyar 'ya'yansu.

Gwamnatin ta Jigawa ta tura wasu daga cikin daliban jihar zuwa kasar ta China domin su yi karatun likita su kuma dawo su bawa jihar gudunmuwa a bangaren kiwon lafiya.

A wani rahoton, kun ji cewa uwar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, ta rufe ofishinta na makonni biyu bayan wasu daga ciki hadimanta sun dawo daga tafiyar da suka yi zuwa Ingila.

Ta kara da bayyana cewa diyarta da ta dawo daga Ingila ta killace kanta, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, wacce ta wallafa wannan ci gaban a shafin na twitter, ta ce ta dau wannan matakin ne don biyayya ga shawarar ministan Lafiya da kuma kwamitin karta-kwana na fadar shugaban kasa a kan cutar Covid-19.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel