Yanzu-yanzu: Coronavirus: Gwamnatin tarayya ta bada umurnin rufe dukkan jami'o'i da makarantun sakandare

Yanzu-yanzu: Coronavirus: Gwamnatin tarayya ta bada umurnin rufe dukkan jami'o'i da makarantun sakandare

Yayinda annobar Coronavirus ke cigaba da yaduwa a duniya, gwamnatin tarayya ta umurci dukkan shugabannin jami'o'i da makarantun sakandare mallakin gwamnatin tarayya su rufe cikin gaggawa.

Gwamnati ta yanke wannan shawara ne domin takaita yaduwar cutar Coronavirus da ta addabi kasashen duniya.

Kawo yanzu, akalla mutane 300 sun kamu da cutar a nahiyar Afrika, yawanci wadanda suka shigo nahiyar daga kasashen Turai da Asiya.

Sakataren din-din-din na ma'aikatar Ilimi, Sonny Echonu, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis inda yace an dauki matakin ne domin kare rayuwar daliban makaranta.

A cewarsa ”Mun umurci dukkan jami'o'i su kulle karshen makon nan, hakazalika Makarantun sakandaren gwanatin tarayyan da suka kammala jarrabawansu. Wadanda basu kammala ba kuma suyi nan da ranar 26 ga Maris, 2020. ”

Yanzu-yanzu: Coronavirus: Gwamnatin tarayya ta bada umurnin rufe dukkan jami'o'i da makarantun sakandare
Yanzu-yanzu: Coronavirus
Asali: Facebook

A wani labarin daban, Kwamishinan lafiya a jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi, ya bayyana cewa sakamakon gwaji ya nuna cewa baturen nan dan kasar Italiya da ya fara shigo da kwayar da cutar Corona cikin Najeriya, ba ya dauke da kwayar cutar yanzu.

Ya bayyana hakan ne yayin wani taro da manema labarai a Legas, kamar yadda jaridar The Punch ta rawaito.

A cewar kwamishinan, za a sake gudanar da gwajin tantancewa na karshe a kan baturen tare da bayyana cewa za a sallame shi da zarar sakamakon gwajin ya sake nuna cewa ba ya dauke da kwayar da cutar.

An fara samun bullar kwayar cutar Coronavirus a ranar 27 ga watan Fabrairu, 2020, bayan baturen dan kasar Italiya da ke aiki a kamfanin simintin na Lafarge ya shigo da ita.

Kazalika, an tabbatar da sake samun kwayar cutar Cronavirus a jikin mutane hudu a jihar Legas a yau, Alhamis.

Kwamishinan lafiya a jihar, Farfesa Akin Abayomi, ne ya sanar da hakan yayin ganawarsa da manema labarai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel