Coronavirus: Diyar Buhari ta killace kanta bayan dawowa daga kasar waje

Coronavirus: Diyar Buhari ta killace kanta bayan dawowa daga kasar waje

Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta sanar da cewa daya cikin 'ya'yan shugaban kasa ta killace kanta bayan dawowa daga kasar Ingila don tabbbatar da cewa ba ta dauke da kwayar da cutar coronavirus.

Uwargidan shugaban kasar ta bayyana hakan ne a cikin wani sako da ta fitar a shafinta na dandalin sada zumunta, tuwita.

"Barka da rana 'yan Najeriya. A yau ne diyata ta dawo daga kasar Ingila, daya daga cikin kasashen da kwayar cutar corona ta mamaya a yankin turai.

"Kamar yadda ministan lafiya na kasa kuma shugaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa a kan kwayar cutar corona ya bayar da shawara, ta killace kanta, ba kuma saboda ta nuna wata alama cewa tana dauke da kwayar cutar Covid-19 ba.

"Ina rokon dukkan iyaye da su yi hakan ga 'ya'yansu idan da bukata, saboda rigakafi yafi magani.

"Kazalika, ina mai bayar da umarnin rufe ofishina cikin gaggawa har na tsawon mako biyu saboda akwai wasu ma'aikatana da suka dawo daga kasar Ingila kwanan nan," a cewarta.

Aisha Buhari ta bayyana cewa ta jinjina wa gwamnonin jihohin arewa maso yamma da na jihar Kwara da Neja bisa yanke shawarar rufe makarantu domin dakile yaduwar kwayar cutar corona.

Kafin wannan rahoto, Legit.ng ta rawaito cewa kwamishinan lafiya a jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi, ya bayyana cewa sakamakon gwaji ya nuna cewa baturen nan dan kasar Italiya da ya fara shigo da kwayar da cutar Corona cikin Najeriya, ba ya dauke da kwayar cutar yanzu.

Ya bayyana hakan ne yayin wani taro da manema labarai a Legas, kamar yadda jaridar The Punch ta rawaito.

A cewar kwamishinan, za a sake gudanar da gwajin tantancewa na karshe a kan baturen tare da bayyana cewa za a sallame shi da zarar sakamakon gwajin ya sake nuna cewa ba ya dauke da kwayar da cutar.

An fara samun bullar kwayar cutar Coronavirus a ranar 27 ga watan Fabrairu, 2020, bayan baturen dan kasar Italiya da ke aiki a kamfanin simintin na Lafarge ya shigo da ita.

Kazalika, an tabbatar da sake samun kwayar cutar Cronavirus a jikin mutane hudu a jihar Legas a yau, Alhamis.

Kwamishinan lafiya a jihar, Farfesa Akin Abayomi, ne ya sanar da hakan yayin ganawarsa da manema labarai.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel