Abinda yasa har yanzu Buhari bai yi jawabi a kan Coronavirus ba - Lai Mohammed

Abinda yasa har yanzu Buhari bai yi jawabi a kan Coronavirus ba - Lai Mohammed

Lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga ‘yan Najeriya a kan annobar coronavirus bai yi ba, cewar ministan yada labarai, Lai Mohammed a ranar Laraba.

Mohammed ya sanar da manema labarai cewa Buhari zai yi jawabi ga jama’ar kasar nan a lokacin da ya dace.

“Idan lokaci yayi , shugaban kasar zai yi jawabi ,” yace.

“Amma, a tunanina abinda kuke son ji daga bakin shugaban kasa shine kuke ji daga garemu. Ba wai kare shugaban kasar muke ba ko kuma kange shi daga maganarku, muna da tabbacin cewa zai yi duk abinda ya dace,” Mohammed yace bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya a ranar Laraba.

Taron majalisar zartarwar ta tarayya ta samu shugabancin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Bayan tabbatar da bullar mugunyar cutar coronavirus, ‘yan Najeriya suna ta kira ga shugaban kasar a kan ya yi jawabi ga ‘yan Najeriya.

‘Yan Najeriya da yawa sun garzaya shafukan na sada zumuntar zamani inda suke ta bukatar jin ta bakin shugaban kasa a kan yadda kasar ta shirya tarbar wannan mugunyar cutar da ta addabi fadin duniya.

Abinda yasa har yanzu Buhari bai yi jawabi a kan Coronavirus ba - Lai Mohammed
Abinda yasa har yanzu Buhari bai yi jawabi a kan Coronavirus ba - Lai Mohammed
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Coronavirus: Diyar Buhari ta killace kanta bayan dawowa daga kasar waje

A yau ne dai gidan talabijin na Channels 24 ya rawaito cewa an tabbatar da samun kwayar cutar Cronavirus a jikin mutane hudu a jihar Legas.

Kwamishinan lafiya a jihar, Farfesa Akin Abayomi, ne ya sanar da hakan yayin ganawarsa da manema labarai. Abayomi ya bayyana cewa an samu mutane hudun ne daga cikin mutane 19 da aka yi wa gwajin kwayar cutar a ranar Laraba.

Ya kara da cewa an kebe mutanen hudu da aka samu da cutar a asibitin cututtuka masu yaduwa da ke Yaba, Legas. Ya ce daga cikin sabbin mutanen da aka samu dauke da cutar akwa wata mata da ta kamu da kwayar da cutar daga wurin mata da ta zo daga kasar Ingila kwana biyu da suka wuce.

A cewarsa, akwai kuma wata mata da ta dawo Najeriya daga kasar Faransa ranar 14 ga watan Maris a jirgin kasar Turkiyya, TK1830.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel