Hukumar yaki da rashawa EFCC ta gurfanar da Saraki a kotu

Hukumar yaki da rashawa EFCC ta gurfanar da Saraki a kotu

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gurfanar da Ope Saraki, dan-uwan tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, a kotu.

EFCC ta gurfanar da Saraki ne kan zargin tafka kudi fiye da kudin aikin kwangiloli biyu da aka bashi lokacin da yake mai baiwa gwamnan jihar Kwara shawara.

Hukumar yaki da rashawa EFCC ta gurfanar da Saraki a kotu

Hukumar yaki da rashawa EFCC ta gurfanar da Saraki a kotu
Source: UGC

KU KARANTA Babu wanda ya kaiwa Kwankwaso hari - Mai magana da yawun Abba Gida-gida

A bangare guda, Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, ya bukaci babban kotun tarayya da ke Legas ta yi fatali da bukatar da hukumar EFCC ta kawo gabanta.

Dr. Bukola Saraki ya bukaci kotu ta yi watsi da karar da EFCC ta kawo inda ta ke bukatar a karbe gidansa da ke Garin Ilorin a jihar Kwara, a mikawa gwamnatin tarayya.

Bukola Saraki ya fadawa kotu cewa bai kamata ta yi amfani da jita-jitar jama’a da ke cewa an gina wadannan gidaje da dukiyar haramun wajen karbe masa dukiyarsa ba.

Lauyan da ya ke tsayawa Abubakar Bukola Saraki watau Kehinde Ogunwumiju SAN, ya roki kotu ta bukaci Jami'an EFCC su kawo hujjar da ke gaskata zargin da ta ke yi.

Babban Lauyan Bukola Saraki Kehinde Ogunwumiju, ya bayyana cewa akwai bukatar hukumar EFCC ta fito da hujja mai gamsarwa kafin a damka mata gidajen har abada.

Lauyan da ke kare tsohon gwamnan Kwara, ya fadawa Alkali mai shari’a Rilwan Aikawa cewa EFCC ba su kawo wata hujjar da za ta sa a mallaka masu gidajen ba.

A Dismaban 2019, EFCC ta samu iznin kotu na karbe wasu gidajen Bukola Saraki da ke Unguwar GRA a Garin Ilorin, da zargin cewa da kudin sata aka gina gidajen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel