Babu wanda ya kaiwa Kwankwaso hari - Mai magana da yawun Abba Gida-gida

Babu wanda ya kaiwa Kwankwaso hari - Mai magana da yawun Abba Gida-gida

Babu wanda ya kaiwa tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jamiyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yayinda ya halarci wani taron siyasa a Kano ranar Laraba, wani hadimin sirikinsa kuma yaronsa, ya laburta.

Mai magana da yawun dan takaran gwamnan jihar Kano na PDP a zaben 2019, Abba Kabir Yusuf, wanda akafi sani Abba Gida-gida, Malam Ibrahim Adam, ya bayyana haka,

Ya ce babu kamshin gaskiya cikin rahoton cewa an kaiwa Kwankwaso hari bayan halartan zama da wakilan uwar jamiyyar PDP kan zabukan shugabannin jamiyyar a Kano.

Babu wanda ya kaiwa Kwankwaso hari - Mai magana da yawun Abba Gida-gida

Babu wanda ya kaiwa Kwankwaso har
Source: Twitter

A jiya an samu rahoton cewa wasu yan daba a Kano sun kai wa ayarin motocin tsohon gwamnan jahar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso hari a ranar Talata, 17 ga watan Maris.

An tattaro cewa an lalata akalla motoci uku a ayarin nasa a lokacin faruwar lamarin wanda ya wakana a kusa da wani otel a birnin Kanon.

An rahoto cewa lamarin ya afku ne jim kadan bayan kwankwaso ya gana da Gwamna Fintiri.

A Wani jawabi daga Ibrahim Adam, kakakin Abba Kabir Yusuf, dan takarar gwamna a zaben Kano na 2019, ya ce: “jigon ya tsira ba tare da rauni ba.”

Adam ya ce: “Yayinda ya ke barin otel din sai wasu yan daba da aka dauko haya suka farma ayarin motocin sanata Kwankwaso Sannan suka lalata motoci uku mallakar wasu yan majalisar dokokinmu.”

Ya Kara da cewa: “Amma Alhamdulillah, anyi taron cikin nasara. Basu cimma abunda suka so ba.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel