Yan Najeriya biyu, mai jego da jaririnta sun kamu da cutar Coronavirus

Yan Najeriya biyu, mai jego da jaririnta sun kamu da cutar Coronavirus

An bayyana wani jariri mai watanni 6 a duniya a matsayin dan Najeriya mafi karancin shekaru da ya kamu da annobar cutar Coronavirus, kamar yadda ministan kiwon lafiya na Najeriya, Osagie Ehanire ya bayyana.

Jaridar Punch ta ruwaito ministan ya bayyana haka ne yayin dayake ganawa da manema labaru a ranar Laraba, 18 ga watan Maris, inda yace jaririn da mahaifiyarsa sun dawo Najeriya ne daga kasar Amurka.

KU KARANTA: Jerin muhimmai matakai 13 da Buhari ya dauka tun bayan shigowar Corona Najeriya

Ministan yace shigowar mutanen biyu daga kasar Amurka inda suka dauko cutar ya kawo adadin yan Najeriya dake dauke da cutar zuwa 8. “Daga cikin sabbin bullar Corona da aka samu, 3 sun dawo ne daga kasar Amurka, yayin da 2 suka dawo daga Birtaniya.

“Muna cigaba da tattara bayanan matafiyan, amma dai mun san mutane daga cikin ukun da suka dawo daga Amurka yan Najeriya ne, uwa da danta, na ukun kuma dan kasar Amurka ne da ya shigo ta iyakar Najeriya, wanda shi ne wanda ya fara shigo da cutar ta kasa ba ta jirgin sama ba, sauran mutane biyu da suk shigo daga Birtaniya duk yan Najeriya ne.” Inji shi.

Ministan ya kara da cewa daga cikin sabbin bullar cutar guda biyar, hudu mazauna jahar Legas ne, sai guda daya dan jahar Ekiti. Sai dai rahotanni sun bayyana cewa Baturen Amurkan da ya shigo da cutar ya mutu.

A wani labarin kuma, kwamitin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa domin yaki da yaduwar cutar Coronavirus a Najeriya ta bayar da shawarar hana baki shigowa daga kasashe 13 na duniya.

Kwamitin ta fitar da sanarwar ne a ranar Laraba, 18 ga watan Maris, inda ta lissafa kasashen da wannan umarni ya shafa kamar haka; China, Italy, Iran, Koriya ta kudu, Spain, Japan, Faransa, Jamus, Norway, Amurka, Birtaniya, Netherlands da kuma Switzerland.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel