Siyasar Najeriya ta zama ‘iya kudin ka iya shagalin ka’ – Inji tsohon gwamna

Siyasar Najeriya ta zama ‘iya kudin ka iya shagalin ka’ – Inji tsohon gwamna

Tsohon gwamnan jahar Ondo na jam’iyyar PDP, Olusegun Mimiko ya koka kan yadda siyasar Najeriya ta zama ‘Iya kudin ka iya shagalin ka’, don haka yace akwai bukatar yi ma tsarin kwaskwarima.

Mimiko ya bayyana haka ne yayin bikin murnar zagayowar ranar haihuwar wani mawakin baitoci mai suna Odia Ofeimun da ya gudana a babban dakin taro na jami’ar jahar Legas a ranar Litinin, 16 ga watan Maris.

KU KARANTA: Gwamnatin Legas ta hana sallar Juma’a na tsawon makonni 4 saboda Corona

Mimiko ya bayyana cewa matsalar kudi a harkar siyasa tasa mutane irin su Odia basu da rawar takawa a cikin siyasar Najeriya saboda basu tara kudi ba. “Idan da haka nan ne, hidimar da ya yi ya isa yasa ya tara kudin da har zai tsaya takara dasu, amma a kasar nan bama mutunta harkar ilimi.

“Idan da mutane kamar su Odia da tarin iliminsu da basirarsu sun samu damar bada gudunmuwa a harkar mulki, da Najeriya tana gab da cimma muradunta gaba daya, idan da gaske muke a Najeriya, da Odia ya zama gwamna a kasar nan, toh amma an sanya kudi a siyasar mu, don haka irinsu basu da wuri.” Inji shi.

Mimiko ya kara da cewa yi ma sauya tsarin mulki a Najeriya ne kadai zai inganta tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya, “Najeriya ba za ta taba cigaba ba har sai an yi mata garambawul.” Inji tsohon gwamnan.

A nasa jawabin, Odia, ya bayyana cewa Najeriya ba ta tsara bukatunta da ayyukanta, wannan ne yasa ba zata taba rabuwa da matsala ba. “Najeriya ta saba da rashin tsara bukatunta, don haka duk mutanen da basu tsara bukatunsu ba, sun tsara faduwarsu kenan.” Inji shi.

A wani labarin kuma, A kokarinta na dakatar da yaduwar cutar nan mai toshe numfashi ta Coronavirus, gwamnatin jahar Legas ta sanar da kulle dukkanin makarantu a duk fadin jahar daga ranar Litinin, 23 ga watan Maris.

Gwamnatin ta bayar da umarnin rufe makarantun gwamnati da makarantun kudi a jahar kamar yadda kwamishinan ilimi, Folashade Adefisayo ta bayyana, inda ta ce matakin ya zama dole don kare malamai da dalibansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel