Majalisa za ta bada umurnin a kamo mata shugaban PPPRA

Majalisa za ta bada umurnin a kamo mata shugaban PPPRA

Majalisar Wakilai na tarayya ta yi barazanar bayar da umurnin a kamo mata babban sakataren hukumar kula da farashin kayan albarkatun man fetur, PPPRA , Mista Abdulkadir Seidu, idan har bai amsa gayyatar da kwamitin kudi na majalisar ta masa ba karo na uku.

Kwamitin ta bukaci ganin shugaban na PPPRA ne saboda rashin biyan kudaden shiga da hukumar ba tayi ba daga shekarar 2014 zuwa 2019 kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kwamitin tana bincikar hukumomi, ma'aikatu da cibiyoyi na gwamnatin tarayya da ba su biyan kudaden shiga cikin asusun gwamnatin tarayya.

Majalisa za ta bada umurnin a kamo mata shugaban PPPRA

Majalisa za ta bada umurnin a kamo mata shugaban PPPRA
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Budurwa ta sa an damke mutumin da ya taba mata nono a motar haya

Shugaban kwamitin, Mista James Falake, ne ya yi wannan barazanar yayin zaman kwamitin na ranar Talata a babban birnin tarayya Abuja bayan ya kori jami'an hukumar da suka zo domin su wakilici shugaban na PPPRA.

Seidu ya ce, saboda haka, muna bukatar ya gabatarwa da kansa a gaban kwamitin a ranar 30 ga watan Maris.

Kazalika, shugaban kwamitin binciken asusun ajiyar hukumomi da ma'aikatu, Mista Wole Oke, a ranar Talata ya gayyaci manajin direkta na hukumar kula da tashohin jiragen ruwa, NPA, Mista Habib Abdullahi da Direktan Kudi na hukumar su bayyana a gaban kwamitin cikin kwanaki bakwai kan rashin yin binciken kwakwaf a asusun na NPA tsawon shekaru hudu.

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar wakilan ta Najeriya ta kuma fara bincike a kan harin da aka kaiwa masu ababen hawa da mazauna kauyen Auno a ranar 9 ga watan Fabrairun 2020.

Kwamitin majalisar a kan rundunar sojin Najeriya, wanda Abdulrazak Namdaz dan jam'iyyar APC daga jihar Adamawa ke shugabanta, ya kira shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai.

Kwamitin na bukatarsa da yayi bayanin abinda ya kai ga harin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel