Matakai 7 da gwamnatin jahar Kaduna ta dauka saboda rugujewar farashi mai da Corona

Matakai 7 da gwamnatin jahar Kaduna ta dauka saboda rugujewar farashi mai da Corona

A sakamakon rushewar farashin gangar danyen mai a kasuwannin duniya wanda hakan ya jefa tattalin arzikin duniya cikin mawuyacin hali, gwamnatin jahar Kaduna ta bullo da wasu matakai domin rage radadin wannan matsala a kan al’ummar jahar.

Hadimin gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai a kan harkar watsa labaru, Muyiwa Adekeke ne ya bayyana haka a ranar Laraba, inda yace gwamnatin ta dauki wannan mataki ne bayan samun rahoton wata kwamiti na musamman da ta kafa wanda ta duba illolin tabarbarewar tattalin arziki da hanyar shawo kan matsalar.

KU KARANTA: Gwamnatin Legas ta hana sallar Juma’a na tsawon makonni 4 saboda Corona

Adekeye yace gwamnatin jahar za ta dauki matakai masu tsauri ta hanyar rage adadin kudaden da za ta kashe wajen ayyukan yau da kullum tare da mayar da hankali a kan aiwatar da manyan ayyuka.

“Duba da yadda manyan kasashen duniya masu karfin tattalin arziki suka kulle kasashenu, hakan na nufin akwai matsalar da Najeriya da ma jahar Kaduna zasu fuskanta a nan gaba kadan da kuma dogon zango, hakan ka iya jefa kasar cikin mawuyacin hali.

“Don haka dole ne jahar Kaduna ta dauki matakan da suka dace tare da aiki da hukumomin gwamnatin tarayya don rage radadin tabarbarewar tattalin arzikin, musamman yadda kudaden da gwamnatin tarayya ke baiwa jahohi zasu ragu, kudin da ake samu daga haraji ma zasu ragu.

“Kudaden da gwamnatin Kaduna ke samu zasu ragu da naira biliyan 17 idan har farashin gangan mai ya tsaya a kan $30 kenan, wanda hakan zai shafi dawainiyar albashin ma’aikata da nay an fansho, manyan ayyuka da kuma ayyukan yau da kullum.” Inji shi.

Matakan da gwamnatin ta dauka sun hada da:

- Mayar da hankali ga gudanar da manyan ayyuka

- Dakatar da tafiye tafiyen jami’an gwamnati zuwa kasashen waje

- Tsaftace hanyoyin kashe kudaden gwamnati

- Za’a cire duk ma’aikacin dake amfani da lambar BVN guda biyu daga jerin yan albashi

- Dakatar da daukan aiki

- Fadada hanyoyin samun kudaden shiga

- Umartar kananan hukumomi su dauki irin wadannan matakai

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel