Gwamnatin Legas ta garkame makarantu saboda annobar Corona

Gwamnatin Legas ta garkame makarantu saboda annobar Corona

A kokarinta na dakatar da yaduwar cutar nan mai toshe numfashi ta Coronavirus, gwamnatin jahar Legas ta sanar da kulle dukkanin makarantu a duk fadin jahar daga ranar Litinin, 23 ga watan Maris.

Jaridar Punch ta ruwaito gwamnatin ta bayar da umarnin rufe makarantun gwamnati da makarantun kudi a jahar kamar yadda kwamishinan ilimi, Folashade Adefisayo ta bayyana, inda ta ce matakin ya zama dole don kare malamai da dalibansu.

KU KARANTA; Gwamnatin Legas ta hana sallar Juma’a na tsawon makonni 4 saboda Corona

“Yana da kyau iyaye su tabbata yaransu suna kauce ma shiga cikin taron jama’a, sa’annan su kasance masu yawan wanke hannuwansu a kai kai a gida, kuma su tabbata sun tsaftace kansu da muhallansu, haka zalika su rike yaransu a gida.

“Matakin kulle makarantun ba shi da nufin tsoratar da jama’a ko kuma jefa su cikin firgici.” Inji ta.

A wani labari kuma, gwamnatin jahar Legas ta sanar da dakatar da gudanar da sallolin Juma’a da taron bauta na Kiristoci a wani mataki na kokarin yaki da yaduwar mugunyar annobar Coronavirus.

Kwamishinan harkokin cikin gida na gwamnatin, Anofiu Elegushi ne ya bayyana haka a ranar Laraba inda yace gwamnatin ta hana duk taro da ya haura mutane 50 a duk fadin jahar.

A cewar kwamishinan, gwamnatin ta dauki wannan mataki ne bayan ganawa da shuwagabannin addinan biyu, ya kara da cewa akwia bukatar jama’a su rage cudanya da juna har sai barazanar annobar ta ragu.

Ya cigaba da cewa: “Wannan dakatarwa na tsawon makonni hudu ne, akwai yiwuwar sake duba umarnin bayan wani dan lokaci, kuma an kafa kwamiti daya kunshi Musulmai da Kiristoci don tabbatar da Masallatai da Coci coci sun bi umarnin.

“Muna kira ga jama’a su dage wajen tsaftace muhallansu tare da wanke hannuwansu a kai akai, haka zalika ya kamata gwamnatin tarayya ta garkame iyakokin Najeriya don hana bakin haure shiga jahar Legas domin yaki da yaduwar cutar, kuma jama’an Legas su kauce ma yin musabaha da juna.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel