Ka yi aiki da wadannan shawarwari 3 cikin gagga wa - Shehu Sani ya yi kira ga Buhari

Ka yi aiki da wadannan shawarwari 3 cikin gagga wa - Shehu Sani ya yi kira ga Buhari

- Shehu Sani ya shawarci shugaban kasa Muhammad Buhari a kan wasu manyan lamurra da ya dace yayi da gaggawa

- Sani yayi kira ga shugaban kasar da ya ziyarci wadanda gobarar fashewar bututun man fetur ta Abule-Ado ya ritsa dasu da kuma mazauna kauyen Kerewa da ke Kaduna

- Tsohon sanatan ya kara da kira ga shugaban kasar da yayi jawabi ga jama'ar kasar a dangane da barkewar mugunyar cutar coronavirus

Tsohon sanata da ya wakilci jihar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijan kasar nan,Shehu Sani, ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan ya gaggauta yin jawabin a kan matsalolin kasar nan.

Tsohon dan majalisar ya bayyana hakan ne a shafinsa na twitter a ranar 18 ga watan Maris. Ya yi kira ga shugaban kasar Najeriya din da yayi jawabi ga jama'ar kasar nan a kan barkewar cutar coronavirus.

Sani ya kara da shawartar shugaban kasar Najeriya da ya kai ziyara ga jama'ar da fashewa bututun man fetur na Abule-Ado ya ritsa dasu a ranar Lahadi, 15 ga watan Maris.

Ya kara da cewa, akwai bukatar shugaban kasar Najeriyan ya kai ziyarar jaje ga jama'ar kauyen Kerew da ke Kaduna inda mutane biyar suka rasa rayukansu sakamakon mummunan aikin miyagu 'yan bindiga.

Ana tsaka da kira ga gwamnatin a kan ta rufe iyakokinta don gujewa yaduwar cutar numfashi ta coronavirus, fadar shugaban kasar ta bayyana matakin da gwamnatin Najeriya ke dauka.

A wani bangare kuma, Legit.ng ta ruwaito cewa biyo bayan yaduwar cutar coronavirus a Najeriya, wasu makarantun kudi a jihar Legas sun rufe duk da kuwa babu wannan umarnin daga ma'aikatar ilimi ta tarayya ko jiha.

Makarantun da suka dauki wannan matakin sun hada da Greenspring da kuma Lagos Preparatory and secondary school, Ikoyi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel