Da duminsa: Gwamnati ba zata kara daukan aiki ba - Ministar Kudi

Da duminsa: Gwamnati ba zata kara daukan aiki ba - Ministar Kudi

Gwamnatin tarayya ta sanya takunkunmi kan daukan aikin yi a ma'aikatun gwamnatin tarayya gaba daya.

Ministar kudi da tattalin arziki, Zainab Shamsuna Ahmed, ta bayyana hakan ne yayinda take hira da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan taron majalisar zantarwa da shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta ranar Laraba.

Ta ce gwamnatin tarayya za ta cigaba da biyan ma'aikata albashi kuma ba zata sallami ma'aikata ba amma ba za'a sake daukan sabbin ma'aikata ba.

Tace“Kan batun daukan aiki, an rigaya da bada umurnin dakatad da daukan aiki. Abinda ma'aikatun keyi dama na maye gurbin wadanda sukayi ritaya an dakatar.“

“Idan abubuwa suka gyaru, zama'aikatuna cigaba. Amma yanzu albashin da zamu biya na da yawa.“

“Shugaban kasa ya bada umurnin cewa a cigaba da biyan albashi da fanshi. Saboda haka bamu tunanin wani rage yawan ma“aikata.“

Zainab ta kara bayani kan matakan da gwamnati ke dauka wajen rage illar annobar Coronavirus kan tattalin arzikin kasa.

Daga cikin matakan shine rage farashin man fetur, gyara kasafin kudin 2020, kara yawan danyen man da aka haka zuwa 2.18 miliyan a rana, canza kudin harajin hukumar kwastam, ayyukan walwala da jin dadi, dss.

KU KARANTA Gwamnatin Legas ta hana sallar Juma’a na tsawon makonni 4 saboda Corona

Da duminsa: Gwamnati ba zata kara daukan aiki ba - Ministar Kudi

Da duminsa: Gwamnati ba zata kara daukan aiki ba - Ministar Kudi
Source: UGC

Gwamnatin tarayya na shawaran rage kasafin kudin Najeriya na 2020 da N1.5 trillion daga N10.59 trillion zuwa N9.09 trillion.

Ministar Kudi, kasafin kudi da shirye-shiryen kasa, Zainab Ahmed Shamsuna, ya bayyana hakan ne ranar Laraba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel