Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya za ta rage kasafin kudin 2020 kuma an fasa daukan sabbin ma'aikata
Gwamnatin tarayya na shawaran rage kasafin kudin Najeriya na 2020 da N1.5 trillion daga N10.59 trillion zuwa N9.09 trillion.
Ministar Kudi, kasafin kudi da shirye-shiryen kasa, Zainab Ahmed Shamsuna, ya bayyana hakan ne ranar Laraba.
Za'a mika wannan bukatar da majalisar dokokin tarayya domin amincewarsu.
Za ku tuna cewa Dirakta Manajan kamfanin man feturin Najeriya NNPC, Mele Kyari, a ranar Laraba ya bayyana cewa akwai barazana ga tattalin arzikin Najerya muddin ba a shawo kan matsalar faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya da cutar Coronavirus ba.
Yayinda yake jawabi a taron shawo kan lamarin da gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele, ya shirya, Kyari ya ce cutar Coronavirus da faduwar farashin manyan kalubale ne ga tattalin arzikin kasa.
An shirya zaman ne bayan farashin man fetur a kasuwar duniya ya sauko daga $57 zuwa $30 ga gangan.
A jawabin, ya ce a yanzu haka, akwai jirgaen ruwa 12 dauke da iskar gas na sayarwa amma babu masu saya saboda faduwar farashin da kuma cutar Coronavirus.
Ya ce na danyen man fetur ya fi muni saboda ”a yau, akwai jiragen ruwa 50 dauke da danyen mai amma basu samu sauka ba.”
”Hakan na nufin cewa yan kasuwan mai basu san inda zau kai danyen man ba. A jiya, kasar Iraqi ta rage farashin man ta da $5 yayinda kasar Saudiyya ta rage na ta da $8.”
”Saboda haka idan kana sayar danyen man ka a farashin $30 sannan ka rage da $8, ka ga $22 ya rage kenan.”
”Wannan babban matsalan zai iya sauki ga kasashe masu tace man fetur irinsu Saudiyya,.. amma ba zai taba yiwuwa ba a Najeriya.”
”Saboda haka ku shiryawa matsala na tsawon watanni 3, ko da farashin ya koma $58, akwai bashin da sai an biya na mai.”
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng