Gwamnatin Legas ta hana sallar Juma’a na tsawon makonni 4 saboda Corona

Gwamnatin Legas ta hana sallar Juma’a na tsawon makonni 4 saboda Corona

Gwamnatin jahar Legas ta sanar da dakatar da gudanar da sallolin Juma’a da taron bauta na Kiristoci a wani mataki na kokarin yaki da yaduwar mugunyar annobar Coronavirus.

Daily Trust ta ruwaito kwamishinan harkokin cikin gida na gwamnatin, Anofiu Elegushi ne ya bayyana haka a ranar Laraba inda yace gwamnatin ta hana duk taro da ya haura mutane 50 a duk fadin jahar.

KU KARANTA: Hukumar JAMB ta canza hanyar da ake bi domin duba sakamakon jarabawa

A cewar kwamishinan, gwamnatin ta dauki wannan mataki ne bayan ganawa da shuwagabannin addinan biyu, ya kara da cewa akwia bukatar jama’a su rage cudanya da juna har sai barazanar annobar ta ragu.

Ya cigaba da cewa: “Wannan dakatarwa na tsawon makonni hudu ne, akwai yiwuwar sake duba umarnin bayan wani dan lokaci, kuma an kafa kwamiti daya kunshi Musulmai da Kiristoci don tabbatar da Masallatai da Coci coci sun bi umarnin.

“Muna kira ga jama’a su dage wajen tsaftace muhallansu tare da wanke hannuwansu a kai akai, haka zalika ya kamata gwamnatin tarayya ta garkame iyakokin Najeriya don hana bakin haure shiga jahar Legas domin yaki da yaduwar cutar, kuma jama’an Legas su kauce ma yin musabaha da juna.” Inji shi.

A nasa jawabin babban limamin jahar Legas, Oluwatoyin Abou-Nollah ya bayyana matakin da gwamnatin ta dauka a matsayin abin a yaba, sa’annan ya yi kira ga Musulmai su bi umarnin gwamnati.

Shi ma shugaban kungiyar kiristoci reshen jahar Legas, Alexander Bamgbola yace kungiyarsu ta amince da wannan umarnin gwamnatin, saboda a cewarsa a yanzu ana maganan yadda za’a rayu ne ba maganan addini ba.

A wani labarin kuma, kwamitin shugaban kasa dake yaki da yaduwar cutar Coronavirus ta kafa wata karamar kwamiti wanda za ta tattauna da shuwagabannin addinai daga bangarorin addinin Musulunci da kuma Kiristanci don duba yiwuwar kulle wuraren ibadu.

Ministan watsa labaru, Lai Muhammad ne ya bayyana haka yayin da yake bayar da jawabi game da shirye shiryen kwamitin a gidan talabijin na NTA, inda yace ba kai tsaye gwamnati za ta rufe wuraren ibada ba, har sai ta samu goyon bayan shuwagabannin addinai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel