Tashin hankali: Matar da aka killace kan Coronavirus a Enugu ta mutu

Tashin hankali: Matar da aka killace kan Coronavirus a Enugu ta mutu

Tsohuwar da aka killace a jihar Enugu bayan dawowarta daga kasar waje kan cutar Coronavirus ta mutu a asibiti.

Punch ta tattaro cewa matar ta mutu ne ranar Lahadi tun kafin ma-aikatar kiwon lafiyar jihar su tabbatar ko ta kamu da cutar ko bata kamu ba.

Iyalanta sun bayyanawa manema labarai cewa an kai ta asibitin Colliery Hospital ne inda aka shirya kula da ita amma akayi watsi da ita ba tare da wani kyakkyawan kula ba.

A wasikar da diyarta ta rubutawa gwamnan jihar, Ifeanyi Ugwuanyi, ta yi alhinin yadda aka yiwa mahaifiyarta rikon sakainar kashi wanda ya yi ajalinta.

Tashin hankali: Matar da aka killace kan Coronavirus a Enugu ta mutu

Tashin hankali: Matar da aka killace kan Coronavirus a Enugu ta mutu
Source: UGC

Tace “Ina rubuta wannan wasikar ne a madadin kaina da iyalina kan wata yar shekara 70 da akayi zargin ta kamu da cutar Coronavirus a Enugu a ranar Asabar, 14 ga Maris, 2020.“

“Mara lafiyar wacce mahaifiyata ce ta mutu ranar Lahadi, 15 ga Maris 2020 bayan an tabbatar da cewa ba ta dauke da cutar.“

“Ta dawo Najerya ranar Laraba 11 ga Maris 2020 bayan kwashe watanni 5 a kasar Ingila inda tae ziyartar yaranta.“

“Yayinda take asibitin, yadda ma-aikatan suka kula da ita abin takaici ne. Sun killaceta cikin wani daki mai muni gaske da aka dade da daina amfani dashi.“

“Maihaifiyata ta mutu ne sakamakon rikon sakainar kashi da rashin kyayyakwan shirin gwamnati wajen horar da maaikata da kuma samar da kayayyaki.“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel