Yan daba sun kai wa Kwankwaso hari a Kano

Yan daba sun kai wa Kwankwaso hari a Kano

- 'Yan daba sun kai wa tawagar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso hari a Kano

- Lamarin ya afku ne jim kadan bayan kwankwaso ya gana da Gwamna Fintiri

- An tattaro cewa an lalata akalla motoci uku a ayarin nasa a lokacin faruwar lamarin wanda ya wakana a kusa da wani otel a birnin Kanon

Wasu yan daba a Kano sun kai wa ayarin motocin tsohon gwamnan jahar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso hari a ranar Talata, 17 ga watan Maris.

An tattaro cewa an lalata akalla motoci uku a ayarin nasa a lokacin faruwar lamarin wanda ya wakana a kusa da wani otel a birnin Kanon.

Yan daba sun kai wa Kwankwaso hari a Kano
Yan daba sun kai wa Kwankwaso hari a Kano
Asali: UGC

An rahoto cewa lamarin ya afku ne jim kadan bayan kwankwaso ya gana da Gwamna Fintiri.

A Wani jawabi daga Ibrahim Adam, kakakin Abba Kabir Yusuf, dan takarar gwamna a zaben Kano na 2019, ya ce: “jigon ya tsere ba tare da rauni ba.”

Adam ya ce: “Yayinda ya ke barin otel din sai wasu yan daba da aka dauko haya suka farma ayarin motocin sanata Kwankwaso Sannan suka lalata motoci uku mallakar wasu yan majalisar dokokinmu.”

Ya Kara da cewa: “Amma Alhamdulillah, anyi taron cikin nasara. Basu cimma abunda suka so ba.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisa ta bukaci Buhari ya yi jawabi ga al’umman Najeriya kan coronavirus

A wani labari na daban, mun ji cewa Hukumar sojin saman Najeriya ta bayyana cewa ta kashe yan bindiga da dama a ruwan wutan da tayi musu a Walawa, Yadi da tsaunin Kuduru dake jihar Kaduna.

A jawabin da diraktan yada labaran hukumar, Air Commodore Ibikunle Daramola, ya saki, ya bayyana cewa sun ragargaza sansaninsu da kayayyaki.

Hukumar Sojin saman sun kai wannan harin ne tare da hadin gwiwar hukumar yan sanda da wasu hukumomin tsaron Najerya.

Daramola yace an kai farmakin ne “bayan rahoton leken asiri ya bayyana yadda yan taaddan bayan korar mazauna daga muhallansu, suke cin karansu ba babbaka suna hallaka mutane.“

Yace “Hukumar NAF ta tura jirginta domin ruwan wuta sansanin yan bindiga inda aka lalata gidajensu tare da hallaka da dama cikinsu.“

“Harin jirgin saman ya baiwa sojojin kasa damar shiga cikin garuruwan domin karasa su.“

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel