Dalilin da yasa na ziyarci Buhari - Diri
- Gwamnan jihar Bayelsa, Mista Diri Douye ya kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyara a fadarsa ta Aso Rock da ke babban birnin tarayya Abuja
- Wannan dai shine karo na farko da gwamnan na jam'iyyar PDP ya ke ziyarar shugaban kasar tun bayan da ya kama mulki a watan Fabrairun 2020
- Gwamna Diri Douye ya ce ya ziyarci shugaban kasar ne domin ya gabatar da kansa kuma ya sanar da shi cewa a shirye ya ke ya yi aiki da gwamnatin tarayya domin kawo cigaba da zaman lafiya a jiharsa
Gwamnan jihar Bayelsa, Diri Douye a ranar Talata ya ce ya kai wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara ne domin ya gabatar da kan shi ga shugaban kasar a hukumance.
Douye ya yi bayanin cewa tun lokacin da ya kama aiki a matsayin gwamna a ranar 14 ga watan Fabrairun 2020 jiya (Talata) ce karo na farko da ya ziyarci shugaban kasar a fadarsa ra Aso Villa da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Asali: UGC
DUBA WANNAN: Budurwa ta sa an damke mutumin da ya taba mata nono a motar haya
Bayan kammala taronsa da shugaban kasa misalin karfe 1.39 na rana, ya shaidawa manema labarai na gidan gwamnati cewa a shirye ya ke ya yi aiki tare da gwamnatin tarayya domin tabbatar da zaman lafiya a jiharsa.
Idan ba a manta ba Duoye ya zama gwamnan Bayelsa ne bayan hukuncin kotun koli na kasa a ranar 13 ga watan Fabrairun 2020 da aka soke zababbun 'yan takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Mista David Lyon da mataimakinsa awanni 24 kafin a ranstar da shi.
Gwamnan ya ce, "Tunda na fara aiki a matsayin gwamnan jihar Bayelsa, ban zo na gaishe da uban kasa ba. A yau, gashi na aikata hakan; na zo na ziyarci uban kasar mu kuma domin muyi aiki tare da gwamnatin tarayya domin tabbatar da zaman lafiya da cigaba mai dorewa a jiha ta. Wannan shine dalilin da yasa na ziyarci shugaban kasa a yau."
A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Buhari ya amince da dage bikin wasanni na kasa (NSF) da aka yi wa lakabi da Edo 2020 a matsayin wani mataki na kare yaduwar cutar Coronavirus a kasar.
Ministan Wasanni na Najeriya Sunday Dare ya sanar da cewa za a dage wasanni na kasar da aka shirya yi a Birnin Benin na jihar Edo.
'Yan wasa a dukkan jihohin kasar sun dade suna shirin zuwa Birnin Benin domin hallartar wannan wasannin kafin sanarwar ta fito a ranar Talata 17 ga watan Maris.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng