Yanzu-yanzu: Gwamnati ta hana matafiya daga Amurka, Ingila, Sin, Italiya dss shigowa Najeriya

Yanzu-yanzu: Gwamnati ta hana matafiya daga Amurka, Ingila, Sin, Italiya dss shigowa Najeriya

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa gwamnatin tarayya ta haramtawa matafiya daga kasashe 13 shigowa Najeriya daga yau saboda annobar cutar Coronavirus.

Gwamnatin ta yanke wannan shawara ne domin takaita yaduwar cutar a Najeriya.

Kawo yanzu, mutane uku kacal aka tabbatar da sun kamu da cutar a Najeriya.

Kasashen da aka haramtawa shiga Najerya sune Sin, Italiya, Iran, Koriya ta kudu, Andalus (Spain), Japan, Faransa, Jamu, Amurka, Norway, Ingila, Holand, da Swizalan.

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta bayyana hakan ne da safiyar Laraba, 18 ga Maris, 2020.

Jawabin yace “Gwamnatin tarayya ta hana shigowa kasar ga matafiya daga kasashen Sin, taliya, Iran, Koriya ta kudu, Andalus (Spain), Japan, Faransa, Jamu, Amurka, Norway, Ingila, Holand, da Swizalan.“

“Wadannan sune kasashe masu mutane masu dauke da cutar akalla 1000.“

“Hakazalika, gwamnatin Najerya ta dakatad da baiwa matafiya daga wadannan kasashen biza.“

“Dukkan matafiyan da suka shigo Najeriya gabanin wannan sanarwan za su fuskanci killacewa karkashin luran NCDC da hukumar kiwon lafiya jiragen ruwa.“

Yanzu-yanzu: Gwamnati ta hana matafiya daga Amurka, Ingila, Sin, Italiya dss shigowa Najeriya

Yanzu-yanzu
Source: Twitter

KU KARANTA Mayakan Sojin Sama sun ragargaji yan bindiga a Kaduna (Hotuna)

A bangare guda, Sabon binciken cibiyar kiwon lafiyar kasar Amurka ya bayyana cewa kwayar cutar Coronavirus na iya rayuwa cikin iska da kan abubuwa na tsawon kwanaki da dama.

Masana kimiyan cibiyar da suka gudanar da binciken a dakin bincike a awon Montana sun bayyana cewa mutane na iya kamuwa da cutar ta iska da kuma taba kayayyaki masu datti.

Cibiyar tace “An gudanar da binciken ne ta hanyar daura kwayar cutar kan alatun amfanin yau da kullun a gida ko asibiti kamar yadda zai iya hawa ta hanyar tari ko taba abu idan wani mai dauke da cutar yayi.“

“Sai masanan suka lura da tsawon lokacin da kwayar cutar ya kwashe da rai kan wadannan kayayyaki.“

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel