Coronavirus: Sabon bincike ya nuna cewa ana iya kama cutar ta iska

Coronavirus: Sabon bincike ya nuna cewa ana iya kama cutar ta iska

Sabon binciken cibiyar kiwon lafiyar kasar Amurka ya bayyana cewa kwayar cutar Coronavirus na iya rayuwa cikin iska da kan abubuwa na tsawon kwanaki da dama.

Masana kimiyan cibiyar da suka gudanar da binciken a dakin bincike a awon Montana sun bayyana cewa mutane na iya kamuwa da cutar ta iska da kuma taba kayayyaki masu datti.

Cibiyar tace “An gudanar da binciken ne ta hanyar daura kwayar cutar kan alatun amfanin yau da kullun a gida ko asibiti kamar yadda zai iya hawa ta hanyar tari ko taba abu idan wani mai dauke da cutar yayi.“

“Sai masanan suka lura da tsawon lokacin da kwayar cutar ya kwashe da rai kan wadannan kayayyaki.“

Coronavirus: Sabon bincike ya nuna cewa ana iya kama cutar ta iska
Coronavirus: Sabon bincike ya nuna cewa ana iya kama cutar ta iska
Asali: Facebook

A bangare guda, Hukumar bautan kasa ta Najeriya, NYSC, ta garkame dukkanin sansanonin horas da yan bautan kasa dake fadin Najeriya a wani mataki na gaggawa don gudun yaduwar annobar cutar Coronavirus a tsakanin matasan.

Premium Times ta ruwaito rukunin farko na yan bautan kasan sun fara samun horo a sansanonin NYSC dake fadin jahohin Najeriya ne a ranar 10 ga watan Maris, kuma kamata yayi su kwashe kwanaki 21 a sansanonin, amma sai ga shi bayan kwanaki 8 an sallame su.

Da dama daga cikin matasa masu yi ma kasa hidima sun shiga rudani yayin da a tsakar daren Talata aka sanar dasu cewa an kawo karshen horaswan da zasu samu a sansanonin, don haka aka mika ma kowannensu takardar aikin da zai yi, da kuma inda aka tura shi aikin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel