Mayakan Sojin Sama sun ragargaji yan bindiga a Kaduna (Hotuna)

Mayakan Sojin Sama sun ragargaji yan bindiga a Kaduna (Hotuna)

Hukumar sojin saman Najeriya ta bayyana cewa ta kashe yan bindiga da dama a ruwan wutan da tayi musu a Walawa, Yadi da tsaunin Kuduru dake jihar Kaduna.

A jawabin da diraktan yada labaran hukumar, Air Commodore Ibikunle Daramola, ya saki, ya bayyana cewa sun ragargaza sansaninsu da kayayyaki.

Hukumar Sojin saman sun kai wannan harin ne tare da hadin gwiwar hukumar yan sanda da wasu hukumomin tsaron Najerya.

Daramola yace an kai farmakin ne “bayan rahoton leken asiri ya bayyana yadda yan taaddan bayan korar mazauna daga muhallansu, suke cin karansu ba babbaka suna hallaka mutane.“

Yace “Hukumar NAF ta tura jirginta domin ruwan wuta sansanin yan bindiga inda aka lalata gidajensu tare da hallaka da dama cikinsu.

“Harin jirgin saman ya baiwa sojojin kasa damar shiga cikin garuruwan domin karasa su.“

“An hallaka akalla kwamandojin Ansaru 5 da yan bindiga dozin daya a harin.“

Kalli hotunan

Mayakan Sojin Sama sun ragargaji yan bindiga a Kaduna (Hotuna)

Mayakan Sojin Sama sun ragargaji yan bindiga a Kaduna (Hotuna)
Source: Facebook

A bangare guda, Ministan kula da al’amuran Yansandan Najeriya, Muhammad Dingyadi ya bayyana cewa nan bada jimawa ba hukumar Yansanda za ta fara daukan sabbin kuratan Yansanda 10,000 a duk fadin Najeriya.

Punch ta ruwaito hakan na daga cikin cika alkawarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka na samar da sabbin jami’an Yansanda 40,000 a tsawon shekaru hudu na wa’adin mulkinsa.

KU KARANTA: Annobar Lassa ta halaka mutane 8, babban Likita da wani hakimi a jahar Bauchi

Dingyadi ya bayyana cewa sun fara tsara yadda daukan aikin zai kasance, wanda suke sa ran zai kara adadin jami’an Yansandan Najeriya tare da taimakawa wajen shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi kasar.

Minista Dingyadi ya bayyana haka ne a babban birnin tarayya Abuja yayin bikin kaddamar da littafi mai suna; “Introduction to law enforcement: A training guide for the Nigeria Police Force.’ Wanda AIG Adeyemi Ogunjemilusi mai ritaya ya wallafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel