Batan N36.8m a hukumar JAMB: An gano 'macizan' da suka wawure kudin

Batan N36.8m a hukumar JAMB: An gano 'macizan' da suka wawure kudin

Wani shaidan EFCC mai suna Stanley Ani a ranar Talata ya fadawa kotun tarayya da ke Abuja yadda jami'an hukumar shirya jarrabawar shiga jami'o'i, JAMB, suka karkatar da zunzurutun kudi har naira miliyan 36.5 daga kudaden shiga da hukumar ta tara.

EFCC ta yi karar wata jami'ar hukumar JAMB, Philomina Chieshe da shugaban ta, Samuel Umoru, shugaban hukumar na garin Makurdi da laifuka takwas da masu alaka da hadin baki, cin amana da almundahana.

Ana tuhumarsu da hadin baki wurin karkatar da kudade mallakar hukumar JAMB daga Augustan 2014 zuwa Yulin 2016 wanda hakan ya saba wa sashi na 9 (2) na Penal Code.

Sai dai mutanen biyu sun musanta aikata laifukan da ake tuhumarsu da shi.

Batan N36.8m a hukumar JAMB: An gano 'macizan' da suka wawure kudin
Batan N36.8m a hukumar JAMB: An gano 'macizan' da suka wawure kudin
Asali: Depositphotos

Da ya ke bayar da shaida a gaban kotun a matsayinsa na shaida na hudu, Ani ya shaidawa kotu cewa ya binciki asusun ajiyar wasu bankunan zamani biyu mallakar wadanda ake zargin.

Ga abubuwan da ya ce sun gano.

"Mun gano cewa an saka jimlar naira miliyan 29 a asusun banki na Chieshe tsakanin Janairun 2014 zuwa Fabrairun 2017.

DUBA WANNAN: Budurwa ta sa an damke mutumin da ya taba mata nono a motar haya

"Daga cikin kudin naira miliyan 2 albashinta ne da wasu allawus na kungiyoyin adashi na JAMB.

"Mun kuma gano cewa naira miliyan 26.9 kudade ne da aka saka mata a asusun sakamakon sayar da katunan duba jarrabawar JAMB.

"Daga asusun ta mun gano cewa ba ta tura kudi zuwa asusun JAMB ba sai dai kusan dukkan kudaden an cire su ne ta hanyar amfani da na'urar ATM," in ji shi.

Mista Ani ya shaidawa kotu cewa Mss Chieshe ta gabatar da takardun shaidan banki da ke nuna ta saka kudaden a asusun bankin shugaban ta, Mista Umoru kamar yadda ya umurce ta bayan an gama siyar da katin na JAMB.

Lauyan wadanda suka shigar da kara, Ekene Iheanocho ya gabatar wa kotu takardun a matsayin hujja.

Bayan ya duba takardun, lauyan Umoru, A.I. Ihejirika ya ce babu takamamen inda aka rubuta cewa kudaden na sayar da katin jarrabawar JAMB ne.

Bayan Mista Ani ya fadawa kotu sakamakon binciken da ya yi, Mai shari'a Peter Affen ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 1 ga watan Yuni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel