Annobar Corona: Hukumar NYSC ta kulle sansanonin horas da yan bautan kasa

Annobar Corona: Hukumar NYSC ta kulle sansanonin horas da yan bautan kasa

Hukumar bautan kasa ta Najeriya, NYSC, ta garkame dukkanin sansanonin horas da yan bautan kasa dake fadin Najeriya a wani mataki na gaggawa don gudun yaduwar annobar cutar Coronavirus a tsakanin matasan.

Premium Times ta ruwaito rukunin farko na yan bautan kasan sun fara samun horo a sansanonin NYSC dake fadin jahohin Najeriya ne a ranar 10 ga watan Maris, kuma kamata yayi su kwashe kwanaki 21 a sansanonin, amma sai ga shi bayan kwanaki 8 an sallame su.

KU KARANTA: Annobar Lassa ta halaka mutane 8, babban Likita da wani hakimi a jahar Bauchi

Annobar Corona: Hukumar NYSC ta kulle sansanonin horas da yan bautan kasa

Annobar Corona: Hukumar NYSC ta kulle sansanonin horas da yan bautan kasa
Source: Instagram

Da dama daga cikin matasa masu yi ma kasa hidima sun shiga rudani yayin da a tsakar daren Talata aka sanar dasu cewa an kawo karshen horaswan da zasu samu a sansanonin, don haka aka mika ma kowannensu takardar aikin da zai yi, da kuma inda aka tura shi aikin.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito matasa yan yi ma kasa hidima sun bayyana cewa jami’an hukumar NYSC sun shaida musu dalilin daukan wannan mataki shi ne sakamakon yaduwar cutar Coronavirus, wanda a yanzu haka ya ta’azzara.

“Da misalin karfe 1 na dare aka fara bamu takardun zuwa wuraren da zamu yi aikin yi ma kasa hidima.” Inji wani dan bautan kasa dake sansanin NYSC a garin Jos. Shi kuma wani dake jahar Gombe yace da sanyin safiyar Laraba aka fara basu nasu takardun.

Sai dai wannan mataki baya rasa nasaba da shawarar da kwamiti na musamman da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa domin yaki da Coronavirus ta bayar, inda ta nemi a daina taron jama’a da dayawa.

Haka zalika kwamitin ta nemi a hana manyan jami’an gwamnati fita kasashen waje, sa’annan ta nemi duk wadanda suka shigo daga kasashen da cutar ta fi kamari sai sun killace kansu na tsawon kwanaki 14, inda za’a sanya idanu a kansu yayin da suke killace.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel