Sarkin Kano ya karbi bakuncin Janar Ali Gusau a fadar masarautar Kano

Sarkin Kano ya karbi bakuncin Janar Ali Gusau a fadar masarautar Kano

Tsohon mashawarcin shugaban kasa a kan harkokin tsaro, Janar Aliyu Gusau ya isa fadar masarautar Kano domin kai ma mai martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ziyarar ban girma.

Ali Gusau ya kai wannan ziyara ga Sarki Aminu Ado Bayero ne da sanyin safiyar Talata, 17 ga watan Maris, inda Sarkin ya yi masa kyakkyawar tarba a wani kebantaccen karamin fada dake cikin gidan sarautar.

KU KARANTA: Annobar Lassa ta halaka mutane 8, babban Likita da wani hakimi a jahar Bauchi

Sarkin Kano ya karbi bakuncin Janar Ali Gusau a fadar masarautar Kano

Sarkin Kano ya karbi bakuncin Janar Ali Gusau a fadar masarautar Kano
Source: Facebook

A hannu guda kuma, a ranar Asabar, 14 ga watan Maris ne mai martaba Sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero ya kai ma dan uwansa mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado ziyarar ban girma a fadarsa tare da nuna mubaya’a.

A wani labarin kuma, Jam’iyyar APC reshen jahar Kano ta shawarci gwamnan jahar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai da ya kirkiri sabuwar masarauta a Kaduna, sai ya nada tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi a matsayin Sarkin sabuwar masarautar.

Sarkin Kano ya karbi bakuncin Janar Ali Gusau a fadar masarautar Kano

Sarkin Kano ya karbi bakuncin Janar Ali Gusau a fadar masarautar Kano
Source: Facebook

A makon da ta gabata ne gwamnan Kaduna ya nada Sunusi cikin kwamitin gudanarwar hukumar zuba hannun jari ta jahar Kaduna, KADIPA, sa’annan washegari ya nada shi uban jami’ar jahar Kaduna, KASU, jim kadan bayan gwamnatin Kano ta tsige shi a matsayin Sarki.

Bugu da kari gwamnan ya kai ma Sarkin ziyara har sabon gidansa dake garin Awe a jahar Nassarawa a ranar da kotu ta bayar da daman sakinsa, inda ya suka yi sallar Juma’a tare, suka rankaya zuwa babban birnin tarayya Abuja har zuwa jahar Legas tare.

Sai dai ashe wannan halacci da gwamnan ya yi ma tsohon Sarkin bai yi ma APC ta Kano dadi ba, inda aka ruwaito mataimakin shugaban jam’iyyar, Alhaji Shehu Maigari ya yi kira ga gwamnan daya nada Sunusin Sarkin Kaduna.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel