Yanzu-yanzu: Buhari ya haramtawa dukkan ma'aikatan gwamnati fita kasar waje

Yanzu-yanzu: Buhari ya haramtawa dukkan ma'aikatan gwamnati fita kasar waje

Gwamnatin tarayya ta haramtawa dukkan ma'aikatanta daga kan ministoci zuwa sakatarorin din-din-din da diraktocin ma'aikatu, tafiya kasar wajen saboda cutar Coronavirus.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana hakan ne ranar Talata yayinda aka rantsar da kwamiti na musamman kan takaita yaduwar Coronavirus.

Hakazalika ya yi kira ga yan Najeriya dake shigowa daga kasar waje su killace kansu na tsawon kwanaki 14 kafin cakuda da jama'a

Mun kawo muku rahoton cewa Akalla kasashen nahiyar Afrika 26 cikin 54 da aka samu bullar annobar cutar Coronavirus kawo safiyar Litinin, 16 ga watan Maris, 2020.

Cutar wacce ke cigaba da yaduwa a fadin duniya ta tayar da hankulan kasashe, ta durkusar da tattalin arzikin duniya tare da karya farashin danyen man fetur a kasuwar duniya.

A fadin duniya yanzu, an tabbatar da mutane 142, 539 sun kamu da cutar kuma 5,393 sun mutu.

A cikin wannan adadin, mutane 80,851 yan kasar Sin ne inda cutar ta samo asali kuma mutane 3,199 sun mutu a can.

Cikin kwanaki biyu na karshen mako, akalla kasashen Afrika 12 sun samu bullar cutar

Ga jerin kasashen nahiyar Afrikan da aka samu bullar yanzu

Algeria, Misra, Tunisiya, Maroko, Senegal, Najerya, Afrika ta kudu, Kamaru, Burkina Faso, Togo, DR Congo, Cote D'Ivoire, Habasha, Kenya, Namibia, Seychelles, Central African Republic, Congo, Equatorial Guinea, Eswatini, Gabon, Guinea, Mauritania, Ruwanda, Ghana da Sudan

A Najeriya, har yanzu mutane biyu aka tabbatar sun kamu da cutar, bayan haka, an gwada mutane 48 a jihohi irinsu Edo, Enugu, FCT, Kano, Lagos, Ogun, Rivers, da Yobe, kuma ba same su da ita ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel