Rikicin APC: Oshiomole ya yafewa Inuwa Abdulkadir da Shuaibu
Shugaban uwar jamiyyar All Progressives Congress, APC, Adams Oshiomhole, ya sanar da yafewa mataimakinsa na yankin Arewa, Lawan Shuaibu, da mataimakinsa na Arewa maso yamma, Inuwa AbdulKadir.
Oshiomole ya yafe musu ne bayan an dakatad dasu daga kwamitin gudanarwan jamiyyar a ranar Talata, 16 ga Maris, 2020 a shelkwatar jamiyyar dake Abuja.
Ya bayyana cewa kwamitin za ta gana da ministan kiwon lafiya, Dakta Osagie Enehire, kan yadda ake fama da lamarin annobar Coronavirus da ta shigo kasar.
A bangare guda, Shugaban jam’iyyar APC mai mulki, kwamared Adams Oshiomole ya bayyana cewa ya dauki muhimmin darasi daga rikita rikitan shugabanci da ta dabaibaye jam’iyyar har ma ta kusan yin awon gaba da shi daga kujerarsa.
Jaridar Punch ta ruwaito Oshimole ya bayyana haka ne a ranar Talata, 17 ga watan Maris yayin da yake gabatar da jawabi a sakatariyar jam’iyyar biyo bayan nasarar wucin gadi daya samu a gaban kotun daukaka kara da ta umarci a bashi daman cigaba da shugabancin jam’iyyar har sai ta kammala sauraron shari’ar.
A cewar Oshiomole zai sauya tsarin shugabancinsa ta yadda zai yi daidai da bulkatar yayan jam’iyyar, haka zalika ya yi kira ga shuwagabannin jam’iyyar su kawar da son ransu, su sanya bukatun Najeriya a gaba.
Don haka ya nemi taron farko na shuwagabannin jam’iyyar ta mayar da hankali wajen tattauna matsalar annobar Coronavirus, Oshiomole ya bayyana haka yayin da yake rike da hannun abokin hamayyarsa, Victor Giadom.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng