Yadda al'amura ke gudana a gidan tsohon sarki Sanusi II Legas bayan mako guda

Yadda al'amura ke gudana a gidan tsohon sarki Sanusi II Legas bayan mako guda

A yau dai mako daya cif kenan da tubabben sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya isa jihar Legas bayan barinsa garin Awe na jihar Nasarawa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ta duba yanayin lamurran da ke faruwa da tsohon sarkin tun bayan isarsa jihar Legas.

A ranar 9 ga watan Maris ne gwamnatin jihar Kano ta tsige sarkin daga karagar mulkin jihar Kano. Bayan nan kuma sai gwamnatin ta tsaresa a jihar Nasarawa.

Tsige rawanin sarkin ya biyo bayan rashin jituwar da ta auku tsakanin Gwamna Abdullahi Ganduje da sarkin tun shekaru biyu da suka gabata. Hakan yasa gwamnan ya fara binciken sarkin a kan waddaka da kudin masarautar.

Kamar yadda sakataren gwamnatin jihar ya bayyana a takardar da yasa hannu ta tuge rawanin sarkin, an tube rawanin sarkin ne saboda rashin biyayya ga dokokin da suka fito daga ofishin gwamnan da sauran cibiyoyin, wadanda suka hada da kin halartar tarukan jihar ba tare da dalili ba.

Tube rawanin sarkin ya kawo karshen zamaninsa ne da yayi tsawon shekaru shida a karagar mulkin masarautar karo na 14. Babu jimawa kuwa gwamnan jihar ya bayyana Aminu Ado Bayero a matsayin madadin sarki Sanusi II.

Yadda al'amura ke gudana a gidan tsohon sarki Sanusi II Legas bayan mako guda

Yadda al'amura ke gudana a gidan tsohon sarki Sanusi II Legas bayan mako guda
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An kama wasu ma'aurata da laifin aikata jima'i a cikin mota

Bayan isar Sanusi birnin Ikko, mutane da dama sun dinga kai masa ziyarar ban girma da jaje.

Kamar yadda daya daga cikin hadimansa yace, Malam Nasiru El-Rufai, Fasto Tunde Bakare, Hadiza Bala Usman da sauransu ne suka fara kai masa ziyara. Daga nan kuwa gidansa ya kasance kamar Makka saboda yadda yake ta samun baki.

Daga cikin manyan bakin da suka ziyarcesa akwai Oba Rilwani Akiolu na jihar Legas wanda ya kai ziyarar tare da wani manyan jiga-jigai.

Shugaban Ovation Group, Dele Momodu ba a barshi a baya ba. Daliban kungiyar dalibai musulmai ta Najeriya sun kai ziyarar ban girma har gida gareshi.

Hakazalika, Mai girma Dan Amar din Kano, Alhaji Aliyu Harazimi da Dr. Bashir Aliyu Umar sun kai masa ziyara. Munir Sanusi, shugaban ma'aikatansa ya ci gaba da karbar bakin a Legas.

Soyayya da kaunar da jama'a ke nuna masa yasa shi mantuwar baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel