Coronavirus: Majalisar wakilai na yunkurin hana sauka ko tashin jirage da taruka

Coronavirus: Majalisar wakilai na yunkurin hana sauka ko tashin jirage da taruka

A yau Talata ne majalisar wakilan Najeriya ta amince da bukatar hana saukar jirage daga kasashen Ingila, Spain, Italiya, Amurka, China da kuma Korea ta Kudu. Hakazalika za ta haramta duk wani taro don hana yaduwar cutar Covid-19.

Ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta duba dakatar da duk sauka da tashin jiragen tare da kuma tarukan don kiwon lafiyar jama'ar kasar nan.

Dan majalisa Luke Onofiok, dan jam'iyyar PDP daga jihar Akwa Ibom ne ya mika bukatar gaban zauren majalisar a ranar Talata. Ya ce gwamnatocin kasashen duniya sun dau matakai don kokarin hana taron da ya kai mutane 50 a wuri daya. Sun kara da karfafa guiwar mutane a kan tsayuwa nesa da juna akalla taku uku tare da tsaftace hannaye.

"Haka kuma ana karfafa guiwar jama'a a kan su zauna cikin gida a duk kasashen da biranen da annobar ta barke. A takaice dai duk ma'aikata ana shawartarsu da su zauna gida kuma dalibai su dinga karatu daga gida a yanar gizo," ya kara da cewa.

Coronavirus: Majalisar wakilai na yunkurin hana sauka ko tashin jirage da taruka
Coronavirus: Majalisar wakilai na yunkurin hana sauka ko tashin jirage da taruka
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Kayattacen hoton tsohon Sarki Sanusi da iyalansa bayan saukarsa daga mulki

Dan majalisar ya gano cewa kusan dukkan wasanni a fadin duniya kamarsu ATP, Judo, gudun famfalaki na London, Formula 1, Kentucky Derby, dambe, da sauransu duk an soke yi ko kuma an dage don gudun ci gaban yaduwar cutar coronavirus.

Kamar yadda ya ce, "Wasannin cikin gidan, makarantun raino har zuwa jami'o'i duk an rufe su tare da cibiyoyin bincike,"

A yau Talata din ne kuwa gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta dage bikin wasanni na jihar Edo da ake yi a garin Benin City saboda tsoron barkewar cutar coronavirus.

Dubban daruruwan 'yan wasa da 'yan kallo kuwa sun shirya tsaf don halartar wannan wasan na Edo2020, duk da ikirarin gwamnatin jihar na cewa ta shirya shawo kan karbar mutane masu yawa kamar hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel