Abinda sabon gwamnan Bayelsa ya fada a kan Buhari bayan ganawarsu a fadar shugaban kasa
A yau, Talata, ne sabon gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, da shugaba Buhari, suka kebe a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya, Abuja.
Da yake magana da manema labarai jim kadan bayan kammala ganawarsu, gwamna Diri ya bayyana cewa wannan shine karo na farko da suka fara hadu wa bayan ya zama gwamna.
Da yake bayyana yadda Buhari ya karrama shi, gwamnan ya ce shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya karbe shi hannu bi-biyu, tamkar yadda uba zai tarbi dan cikinsa.
Ya bayyana cewa ya shirya ziyarar ne domin kulla alakar aiki da zata amfani jama'ar Bayelsa a tsakani gwamnatinsa a matakin jiha da kuma gwamnatin tarayya.
"Tunda na zama gwamnan jihar Bayelsa a ranar 14 ga watan Fabrairu, ban zo na kawo gaisuwa wurin uban kasa ba, sai yau. Na zo domin na gaishe shi a matsayinsa na uba ga kowa da kuma kulla alakar aiki a tsakanin gwamnatin jihar Bayelsa da gwamnatin tarayya.
DUBA WANNAN: An bayyana shirin tsohon sarki Sanusi II na gaba bayan tube rawaninsa
"Shugaban kasa ya karbe ni hannu bi-biyu, tamkar daya daga cikin 'ya'yansa, ya karrama ni matuka. Ya fada min cewa ya ji dadin zuwa na, kuma yana farin ciki da salon mulkin da na fara. Ya sanar da ni cewa ya karanta rahoton da na aika masa, musamman a kan halin tsaro a jihar Bayelsa.
"Ya yi min alkawarin cewa zai yi aiki tare da ni wajen tabbatar da tsaro domin samun zaman lafiya a jihar Bayelsa da yankin Neja Delta," a cewar gwamna Diri.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng