Gobara ta tafka mummunar barna a sakatariyar karamar hukumar Gusau

Gobara ta tafka mummunar barna a sakatariyar karamar hukumar Gusau

Wata gobara da ta tashi da tsakar ranar Talata ta tafka mummunan barna a sakatariyar karamar hukumar Gusau ta jahar Zamfara, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gobarar da kyar da sudin goshi jami’an hukumar kashe gobara ta jahar Zamfara tare da taimakon ma’aikatan karamar hukumar suka ci galaba a kan wutar.

KU KARANTA: Annobar Lassa ta halaka mutane 8, babban Likita da wani hakimi a jahar Bauchi

Sai dai duk da wannan namijin kokari da aka yi wajen kashe wutar, sai da ta kone ofishin mataimakin shugaban karamar hukumar kurmus, sa’annan ta kona ofishin hukumar kula da shige da fice watau Immigration, ofishin daraktan noma da ofishin hukumar wayar da kan jama’a.

Amma jami’an karamar hukumar sun bayyana cewa babu wanda ya mutu ko ya samu rauni a sakamakon gobarar. Alhaji Nura Musa, sakataren karamar hukumar Gusau ya bayyana musabbabin tashin wutar, inda yace matsalar lantarki ne daga wani ofis.

“Babu wanda ya samu rauni, kuma ma’aikatan sun yi namijin kokari wajen rage barnar da gobarar ta shirya tafkawa tun kafin zuwa jami’an kashe gobara, farin cikinmu daya da Allah yasa wutar ta tsaya a iya ofisoshi, amma dai a yanzu bamu da tabbacin iya asarar da muka yi.” Inji shi.

A wani labarin kuma, annobar zazzabin cutar Lassa ta yi sanadiyyar mutuwar wani babban likita dake aiki a cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya na garin Azare na jahar Bauchi, da wani babban hakimi da kuma wasu mutane 8.

Wata majiya mai karfi daga asibitin koyarwa na jami’ar jahar Bauchi ta bayyana cewa wani likita mai suna Mansur Mohammed ya rasu a sanadiyyar zazzabin Lassa a ranar Juma’a, 13 ga watan Maris.

Majiyar ta bayyana cewa Dakta Mansur tare da wata ma’aikaciyar jinya sun kamu da cutar ne bayan kulawa da wani mara lafiya dake dauke da cutar a FMC Azare, daga nan aka garzaya dasu asibitin koyarwa na ATBU.

“Dukansu biyu sun mutu, kuma a yanzu akwai likitoci guda 5 da aka killacesu sakamakon kamuwa da suka yi da cutar.” Kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel