Zan bi masu zabe har gida ina daka musu sakwara har sai naci zabe- Dan takara

Zan bi masu zabe har gida ina daka musu sakwara har sai naci zabe- Dan takara

- Dan takarar kujerar majalisa mai wakiltar Wuogon na Yamma, John Dumelo ya bayyana cewa ba zai daina yakin neman zabe na gida-gida ba har sai ya ci zaben

- Bayan dan wasan kuma mai jinkan mutanen ya wallafa hotunan shi yana dakawa jama'a sakwara a shafinshi na twitter, ma'abota amfani da kafar sada zumuntar zamanin sunyi caa a kanshi

- Amma kuma, John Dumelo ya bada amsar cewa jajircewa da aiki tukuru ne ke bada tabbacin zai yi nasara a zaben don haka ba zai daina wannan salon yakin neman zaben ba

Dan takarar kujerar majalisa mai wakiltar Wuogon na Yamma, John Dumelo ya bayyana cewa ba zai daina yakin neman zabe na gida-gida ba har sai ya ci zaben.

Bayan dan wasan kuma mai jinkan mutanen ya wallafa hotunan shi yana dakawa jama'a sakwara a shafinshi na twitter, ma'abota amfani da kafar sada zumuntar zamanin sunyi caa a kanshi. Sun ce daka sakwara, yin kitso da kuma taya masu zabe aiyukan gida ba zai zama tabbacin cewa za a zabeshi ba.

Zan bi masu zabe har gida ina daka musu sakwara har sai naci zabe- Dan takara
Zan bi masu zabe har gida ina daka musu sakwara har sai naci zabe- Dan takara
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Bana bukatar aure don mahaifina yana lalata dani, bana dana-sani - Budurwa

Amma kuma, John Dumelo ya bada amsar cewa jajircewa da aiki tukuru ne ka bada tabbacin zai yi nasara a zaben don haka ba zai daina wannan salon yakin neman zaben ba.

Kamar yadda yace, zai yi komai da dan Adam zai iya yi don ganin ya samu nasara koda kuwa zai dinga daka wa jama'a sakwara ne.

Akwai abin mamaki idan aka ji dan siyasa na fadin hakan, amma dai zamu kalmashe kafa mu ga abinda gobe za ta haifar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel