Duk lokacin da matata da zage ni, ina kara aure - Wani magidanci mai mata 58

Duk lokacin da matata da zage ni, ina kara aure - Wani magidanci mai mata 58

Wani mai magungunan gargajiya a jihar Enugu mai suna Simon Odo ya bayyana dalilin da yasa ya ke da mata har guda 58.

Da ya ke magana da manema labarai a ranar Litinin, mai maganin ya ce duk lokacin da daya daga cikin matansa da zage shi, ya kan kara auro mata daya, ya kara da cewa maza da yawa su kan mutu da kuruciyarsu ne domin tayar musu da hankali da matansu ke yi.

Ya ce, "Duk lokacin da daya daga cikin mata na ta zage ni, sai in karo aure. Ba zan lamunci mata su rika zagi na ba.

"Misali, Idan maza 20 sun mutu a Najeriya, biyar ne cikinsu kawai suka yi mutuwar Allah da annabi. Sauran 15 din sun mutu ne sakamakon rabuwa da matansu da halaye marasa kyau na matan. Haka yasa duk lokacin da mace da zage ni sai in kara aure."

Duk lokacin da matata da zage ni, ina kara aure - Wani magidanci mai mata 58
Duk lokacin da matata da zage ni, ina kara aure - Wani magidanci mai mata 58
Asali: Twitter

Da aka masa tambaya kan yadda ya ke hidima da iyalansa, Odo ya ce Ubangiji bai yi kuskure ba da ya bashi yara masu tawa domin shi ke kula da hallitunsa.

DUBA WANNAN: Shugabar wurin aikin mu ta kori ne don na ki yin zina da ita - Matashi

"Ubangiji ya yi watsi da mutane saboda muggan ayyukan da su ke aikatawa. Ba ya amsa addu'o'insu saboda ba mu kaunan junan mu. Yara ba su yi wa na gaba da su biyayya. A zamanin da mu kan girmama na gaba da mu.

"Mu hudu ne, mutane da ke damfarar al'umma. Na farko shine Ubangiji, na biyu shine Yesu almasihu; Sai sarauniyar teku da ni, sai kuma sarkin Shedanu. Mutane da dama suna ikirarin cewa ni mahaifinsu ne kuma za su iya warkar da mutane.

"Maganan gaskiya, ban koyar da kowa ba harkar magungunan gargajiya saboda haka wadannan mutanen 'yan damfara ne.

"Mutane suna yawo suna ikirarin cewa Ubangiji ya sanar da su wasu abubuwa suna kuma amshe kudaden mutane. 'Yan damfara ne ya kuma kamata mutane su farga su dena kula su."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel