Karfin hali: Yadda fasinja ya sace wa direban mota wayar salula da N20,000

Karfin hali: Yadda fasinja ya sace wa direban mota wayar salula da N20,000

An gurfanar da wani fasinja dan shekara 27, Tolu Omini-Ekpo a ranar Talata a gaban kotun Majistare da ke Tinubu a Legas kan zarginsa da sace wa direban tasi wayar salula da kudinta ya kai N76,000 da kuma N20,000 kudin mota.

'Yan sanda sun tuhumar Omini-Ekpo da laifin sata.

Amma bai amsa laifin da ake tuhumarsa da shi ba.

Mai shigar da kara, Sufeta Ajaga Agboko ya shaidawa kotu cewa wanda aka yi karar ya aikata laifin a ranar 9 ga watan Maris misalin karfe 2 na rana a Eko Hotel and Suite da ke titin Adetukumbo Ademola a Victoria Island a Legas.

Karfin hali: Yadda fasinja ya sace wa direban mota wayar salula da N20,000

Karfin hali: Yadda fasinja ya sace wa direban mota wayar salula da N20,000
Source: Twitter

Ya yi ikirarin cewa wanda aka yi karar ya sace waya kirar Tecno da kudinta ya kai N76,000 da kuma N20,000 mallakar direban tasi din Mustapha Adebayo.

Mista Agboko ya yi ikirarin cewa wanda akayi karar ya tambayi direban ya bashi aron wayarsa domin ya yi amfani da manhajar lissafi daga nan kuma ya tsere bayan an tsaya inda zai sauka.

DUBA WANNAN: Shugabar wurin aikin mu ta kori ne don na ki yin zina da ita - Matashi

Mista Agboko ya kuma kara da cewa wanda aka yi karar ya kuma sace wata Infinix da kudinta ya kai N46,000 mallakar wani Mista Moses Okedeji.

Mista Agboko ya ce laifin ya sabawa dokokin jihar Legas sashi na 287 na shekarar 2015.

Shugaban kotun, Majistare T.A. Anjorin-Ajose ya bayar da belin wanda aka yi karan kan kudi N20,000 tare da mutane biyu da za su karbi belinsa.

Ya kuma dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 6 ga watan Afrilu kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel