An hana masu shayi, yan babur, masu suya wuce karfe 11 na dare a Sokoto

An hana masu shayi, yan babur, masu suya wuce karfe 11 na dare a Sokoto

A ranar Litinin, hukumar yan sanda a jihar Sokoto ta alanta hana hawa babur da keke a daidaita sahu a jihar daga karfe 11 na dare zuwa 6 na safe.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, ASP Mohammed Sadiq Abubakar, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki madadin kwamishanan yan sandan jihar, Ibrahim Sani Kaoje.

A cewarsa, hukumar ta dau wannan matakin ne domin samun cigaba wajen nasarorin da ake samu wajen yakan fashi da makami, garkuwa da mutane, da hare-haren yan bindiga a jihar.

Ya kara da cewa dukkan masu shayi da sayar da Suya su rife dandalinsu fari daga karfe 11 na dare zuwa 6 na safe.

Wakilin Vanguard ya ziyarci teburan masu shayi da Suya domin tabbatar da yadda mutane ke biyayya ga sanarwar kuma ya bayyana cewa lallai mutane sun yi biyayya.

A hira da wani mai shago, yace ”Na samu labarin dokar kuma ba zan yarda a kamani ba, ka san yadda yan sandanmu suke, suna son amfani da kowace dama.”

An hana masu shayi, yan babur, masu suya wuce karfe 11 na dare a Sokoto

An hana masu shayi, yan babur, masu suya wuce karfe 11 na dare a Sokoto
Source: UGC

Za ku tuna cewa a ranar 20 ga watan Janairu ne gwamnatin jihar ta haramta amfani da babura da daddare a jihar. Ta ce an dauki matakin ne domin inganta tsaro a jihar.

Wasu daga cikin mutane da suka bayyana ra'ayoyinsu sun ce dokar tana janyo musu wahalhalu domin babura suke amfani da shi don zirga-zirga a jihar.

Wani mai sanaar achaba Yusif Mohammed ya ce "Kudin da na ke samu ya ragu sosai saboda galibi da daddare na ke aikin jigilar fasinja da kayayyaki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel