Mahaifiya ta garkame diyarta a bandaki na shekaru bayan fasto yace mayya ce

Mahaifiya ta garkame diyarta a bandaki na shekaru bayan fasto yace mayya ce

- Kungiyar yaki da cin zarafin kananan yara ta ceto wata yarinya mai shekaru 13 daga kangin rayuwar da ta shiga

- Yarinyar ‘yar asalin Oron ce da ke jihar Akwa Ibom, an gano cewa mahaifiyarta ce ta garkameta a bandaki na shekaru

- Mahaifiyar tayi hakan ne bayan da faston cocinsu ya zargi yarinyar da zama mayya kuma tana dauke da miyagun aljanu

An ceto wata yarinya mai shekaru 13 wacce ta dau shekaru tana shan wahala a hannun mahaifiyarta. An zargi mahaifiyarta da garkameta a cikin bandaki, azabtar da ita tare da hana ta abinci sakamakon ikirarin da tayi na zama mayya kuma ragowar miyagun aljanu. Lamarin ya faru ne a Oron, jihar Akwa Ibom.

Kamar yadda kungiyar kare hakkin kananan yara ta sanar, yarinyar da aka gano sunatan ta Mercy Effiong an garkameta ne a bandaki mai matukar duhu bayan fasto ya ce tana dauke da miyagun aljanu.

Mahaifiya ta garkame diyarta a bandaki na shekaru bayan fasto yace mayya ce

Mahaifiya ta garkame diyarta a bandaki na shekaru bayan fasto yace mayya ce
Source: Twitter

KU KARANTA: Nayi bakin cikin kashe mutum daya, na so kashe dukkan makwabtana ne - Wanda ake zargi

An gano cewa Mercy ba ta samun abinci kuma tana cin kashi da shan fitsarinta ne don rayuwa.

Mahaifiyarta ta manta da ita sakamakon wannan ikirarin da faston cocinsu yayi. Ba wannan bane karo na farko da aka taba samun iyaye na yi wa yaransu hakan. Sau da yawa sai yaran sun rasa rayukansu sannan ake gano musabbabin lamarin.

Mercy ‘yar asalin Oron ce da ke Akwa Ibom, yankin da aka gano sun kware wajan daukar camfi don azabtar da yaransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel