Zan iya auren duk yawan matan da nake so don ni Musulmi ne - Tsohon dan majalisar tarayya
- Fitaccen dan siyasa kuma hamshakin mai arziki, Ned Nwoko ya bayyana cewa yana da damar aurar ko mata nawa yaso
- Ya ce ba zai taba dana-sani ko bada hakuri ba kan ya aura matar da yake so, komai kuwa tazarar shekarunsu
- Babban mai kudin ya bayyana cewa shi jinin sarauta ne don haka yana da nasaba da kuma kudin da zai iya rike mata da yawa
Biloniya Ned Nwoko mijin tsohuwar jarumar fina-finai Regina Daniels ya bayyana cewa shi Musulmi ne. A don haka addini ya amince mishi da ya auri mata da yawa kamar yadda yake so, kamar yadda jaridar Gistmania ta wallafa.
Hakazalika babban mai kudin ya bayyana cewa shi jinin sarauta ne don haka yana da kudi da kuma nasabar da za ta bar shi tara mata ko nawa yake so.

Asali: Instagram
KU KARANTA: Nayi bakin cikin kashe mutum daya, na so kashe dukkan makwabtana ne - Wanda ake zargi
Dan siyasar ya bayyana hakan ne ta wata takarda da mai magana da yawun shi ya fitar. Ya kara da jaddada cewa ba zai taba bada hakuri ba don ya auri matar da yake so da kauna komai kuwa banbancin shekarun da ke tsakaninsu.
Kamar yadda takardar ta ce: ”Alhamdulillahi, Ned Nwoko jinin sarauta ne kuma ko mata nawa yaso zai iya aura. Shi ba yaro bane kuma ya san abinda ya dace da shi. Kada kuma ku manta, Musulmi ne na gari kuma addini ya amince mishi da ya auri ko mata nawa ne. Ba zai so yin tsokaci a kan matar shi Regina Daniels ba a halin yanzu.”
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng