Yadda 'yan kasar Indiya ke shan fitsarin Shanu don maganin Coronavirus

Yadda 'yan kasar Indiya ke shan fitsarin Shanu don maganin Coronavirus

- Wata kungiyar mabiya addinin Hindu da ke kasar Indiya sun hada liyafar shan fitsarin Shanu don kariya daga cutar Coronavirus

- Kwararru sun bayyana cewa fitsarin Shanun baya maganin kowacce cuta har da cutar daji

- Liyafar, wacce kungiyar mai suna Akhil Bharat Hindu Mahasabha ta dauka nauyi, ta samu halartar mutane 200

Wata kungiyar mabiya addinin Hindu da ke kasar Indiya sun hada liyafar shan fitsarin Shanu don garkuwa daga cutar Coronavirus.

Mutane da yawa daga cikin mabiya addinin Hindu din na bautar Shanu ne kuma suna shan fitsarin shi da niyyar ya kare su daga cutuka masu tarin yawa.

Kwararru sun bayyana cewa fitsarin shanun baya maganin kowacce cuta har da cutar daji, kuma babu wata alama da ke bayyana yana maganin cutar Coronavirus din.

Liyafar, wacce kungiyar mai suna Akhil Bharat Hindu Mahasabha ta dauka nauyi anyi a hedkwatartsa da ke babban birnin kasar, ta samu halartar mutane 200. Hakazalika wadanda suka shirya liyafar na fatan shirya irinta a cikin India.

“Muna shan fitsarin shanu tun kusan shekaru 21 da suka gabata. Muna wanka da kashin shima. Bamu taba bukatar amfani da wani maganin bature ba,” Om Prakash yace, wani mutum da ya halarci liyafar.

Yadda 'yan kasar Indiya ke shan fitsarin Shanu don maganin Coronavirus

Yadda 'yan kasar Indiya ke shan fitsarin Shanu don maganin Coronavirus
Source: UGC

KU KARANTA: Nayi bakin cikin kashe mutum daya, na so kashe dukkan makwabtana ne - Wanda ake zargi

Chakrapani Maharaj, shugaban dukkan kungiyoyin mabiya addinin Hindu, ya wallafa hotonsa yayin da yake kai cokali mai cike da fitsarin shanun kusa da fuskarshi a matsayin kariya daga cutar coronavirus din.

Shugabanni daga jam’iyyar Firam Minista Narendra Modi suna ta kara jan hankali tare da kara wa jama’a karfin guiwa a kan amfani da najasar shanun a matsayin maganain cutar kansa.

Kwayar cutar coronavirus din da kama mutane sama da 138,000 a fadin duniya kuma ta halaka mutane a kalla 5,000, bata da magani a halin yanzu. Kuma gwamnatocin kasashen fadin duniya na faman neman yadda za a shawo kan barkewar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel