Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da nasarar Oshiomole jiya

Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da nasarar Oshiomole jiya

Tamkar mage mai rai bakwai, shugaban jamiyyar All Progressives Congress (APC) Adams Aliyu Oshiomole, ya samu nasara kan wadanda sukayi kokarin tunbukesa daga kan kujerarsa.

Wannan shine karo na biyu cikin watanni uku da akayi kokarin kwace masa kujerarsa.

A yau Talata akayi niyyar gudanar da taron majalisar zantarwan jamiyyar domin ciresa amma kotun daukaka kara ta yanke hukuncin hana aiwatar da shariar dakatad da shi.

Gabanin haka, shugaba Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin APC kuma sun yanke shawarar cewa a daga zaman majalisar zantarwar.

Ga abubuwa 5 da mka sani game da lamarin:

1. A yanzu dai da wuyan Adams Oshiomole ya ciru

Tun ranar 4 ga Maris da kotu ta dakatad da shi, Sakataren jamiyyar, Victor Giadom, ya yi kokarin ganin cewa an nadashi mukaddashin shugaban APC amma yanzu da Oshiomole ya dawo, Victor ya yi biyu babu - Babu kujerar shugaba kuma babu na sakatare saboda Oshiomole zai rantsar da Bulama matsayin sabon Sakataren.

2. An dakatad da zaman majalisar zantarwar APC gaba daya

A ganawar Buhari da gwamnonin APC, sun yanke shawarar dakatad da zaman majalisar zantarwa NEC gaba daya. hakan na nuna cewa babu yadda Oshiomole zai ciru kenan.

3. Cibaya ga wadanda ke kokarin tsige Oshiomole

Wadanda ke kokarin tsige Oshiomole musamman gwamnoni sun samu cibaya, musamman Kayode Fayemi (Ekiti); Nasir El-Rufai (Kaduna); Godwin Obaseki (Edo); Abubakar Bagudu (Kebbi); Muhammad Badaru Abubakar (Jigawa) da Yahaya Bello (Kogi).

An bayyana cewa wadannan gwamnonin na kokarin ganin bayan Oshiomole ne saboda zaben 2023.

Yayinda gwamnan Ekiti, Fayemi, ke neman kujerar mataimakin shugaban kasa a 2023, El-Rufai da Bagudu na kokarin takarar kujerar shugaban kasa. Shi kuma Obaseki na son zarcewa matsayin gwamnan Edo.

4. Nasara ga masu goyon bayan Oshiomole

Gwamnoni masu goyon bayan Oshiomole irinsu Babajide Sanwo-Olu (Lagos); Gboyega Adegboyega (Osun); Dapo Abiodun (Ogun); Hope Uzodinma (Imo); Aminu Masari (Katsina); Abdullahi Sule (Nasarawa) and Babagana Zulum (Borno) na farin ciki a yanzu.

5. Obaseki na cikin halin ha'ula'i

Gwamnan jihar Edo ya kasance mutum mafi farin ciki yayinda kotu ta dakatad da Oshiomole. Bayan haka, ya shirya zaman maye Oshiomole da Victor Giadom. Amma yanzu da Oshiomole ya dawo, wani hali yake ciki?

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel