Kayattacen hoton tsohon Sarki Sanusi da iyalansa bayan saukarsa daga mulki

Kayattacen hoton tsohon Sarki Sanusi da iyalansa bayan saukarsa daga mulki

Daya daga cikin 'ya'yan tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, Ashraf Sanusi ya wallafa wani hoton 'yan gidansu a shafinsa na Instagram kwanaki kadan bayan sauke mahifinsa daga sarautar Kano.

Bisa alamu an dauki hoton ne a gidan Sanusi da ke Legas inda ya koma bayan kotu ta bayar da umurnin a bashi izini ya yi walwala ya tafi duk inda ya ke so a maimakon tsare shi da aka yi a jihar Nasarawa.

Mutane da dama suna ta kai wa tsohon sarkin ziyara a Legas cikinsu har da sarkin Legas.

Hoton Sanusi da iyalansa bayan saukarsa daga mulki

Hoton Sanusi da iyalansa bayan saukarsa daga mulki
Source: Twitter

A cikin wata hirar bidiyo da ta bazu a kafafen sada zumunta, Sanusi II ya bayyana cewa bai yi nadamar abinda ya faru ba domin ya san cewa komi kaddara ne daga Allah daman Allah ya kaddara ranar da zai zama Sarki da kuma ranar da zai sauka daga sarautar.

Ya kuma ce zai cigaba da ayyukansa kamar yadda ya saba na yin lakcoci, da bayar da shawarwari a wasu hukumomi na kasa da ma kasashen ketare kawai dai ba zai rika hawa doki bane sosai kamar yadda Sarki ke yi.

Ya mika godiyarsa da 'yan uwa da al'umma bisa goyon baya da suka ba shi tare da kira ga al'ummar Kano su bayar da goyon baya tare da yi wa sabon sarki, Aminu Ado Bayero biyayya.

DUBA WANNAN: Kwankwaso: Ina farin ciki domin wadanda suka yi garkuwa da Sanusi sun sake shi

Hoton Sanusi da iyalansa bayan saukarsa daga mulki

Hoton Sanusi da iyalansa bayan saukarsa daga mulki
Source: Twitter

A wani rahoton, kun ji cewa a ranar Litinin ne Gungun Sarakunan kasar Ibadan wadanda ake kira Mogajis su ka gargadi Mai girma gwamnan Ekiti game da shirin da ya ke yi na tsige Sarakunan jiharsa.

Sarakunan gargajiyar sun ja kunnen gwamna Kayode Fayemi da cewa ka da ya sake ya kawo masu bakuwar dabi’a a wannan zamani na tunbuke masu mulki a kasar Yarbawa.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust, wadannan masu iko sun bayyanawa gwamnan na APC cewa tsige Sarakunansa 11 ya na da hadari a kasar ta Yamma. Manyan Sarakan sun yi magana ne ta bakin Mai magana da yawunsu watau Cif Wale Oledoja wanda ya tunawa gwamnonin Ekiti da Kano cewa wa’adinsu fa kayyadadde ne.

Wale Oledoja ya ce yayin da gwamnoni irin Kayode Fayemi da Abdullahi Ganduje ba su iya zarce shekaru takwas a kan mulki, Sarakuna kuwa su na iko ne har sai sun bar Duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel