Nayi bakin cikin kashe mutum daya, na so kashe dukkan makwabtana ne - Wanda ake zargi

Nayi bakin cikin kashe mutum daya, na so kashe dukkan makwabtana ne - Wanda ake zargi

- Wani matashi da ake zargi da kisan kai mai shekaru 27 mai suna Ejike Eze, ya bayyana rashin jin dadinsa na kasa kashe dukkan makwabtan shi

- Dan asalin jihar Ebonyi din da ke zama a yankin Ayegbami da ke Ijebu Ode na jihar Ogun yana sana’ar kyadi ne tun bayan saukar shi a garin

- Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ne suka damke Eze bayan an zarge shi da sokawa wata makwabciyar shi wuka bayan ta zarge shi da satar wayarta

Wani matashi da ake zargi da kisan kai mai shekaru 27 mai suna Ejike Eze, ya bayyana rashin jin dadinsa na kasa kashe dukkan makwabtan shi a jihar Ogun.

Dan asalin jihar Ebonyi din da ke zama a yankin Ayegbami da ke Ijebu Ode na jihar Ogun, yana sana’ar kyadi ne tun bayan saukar shi a garin. Gidan da yake zaune kuwa ya cika ne da ‘yan kabilar Yoruba da Igbo.

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ne suka damke Eze bayan an zarge shi da sokawa wata makwabciyar shi wuka bayan ta zarge shi da satar wayarta.

Lamarin kuwa ya auku ne a ranar Juma’a da ta gabata.

An gano cewa, Eze da matar da ta rasu mai shekaru 59 sam basu jituwa amma sai a ranar ta zarge shi da satar wayarta.

Fusatar da ya yi da lamarin ne yasa ya kai mata hari inda ya kasheta tare da guduwa. Bayan kwanaki biyu kuwa sai ‘yan sanda suka damke shi a tashar motar Ijebu Ode yana shirin barin garin.

Nayi bakin cikin kashe mutum daya, na so kashe dukkan makwabtana ne - Wanda ake zargi
Nayi bakin cikin kashe mutum daya, na so kashe dukkan makwabtana ne - Wanda ake zargi
Asali: UGC

KU KARANTA: Machina: Gari a arewa da macizai ke da dangantaka mai kyau da mutane

A yayin da manema labarai suka bukaci jin ta bakin wanda ake zargin a hedkwatar ‘yan sandan da ke Eleweran, ya bayyana a fusace. An garkame shi ne a sashi na musamman na bincikar laifukan kisan kai don bincike tare da gurfanarwa.

Ya zargi dukkan makwabtan shi da yaransu da zama makiyan shi kuma bai ji dadi ba da bai kashesu duka ba. “Ina garkame ne saboda kisan kai da nayi. Na soki makwabciyata ce wacce ba zan iya tuna sunanta ba. Muna zama a gida daya ne da ke yankin Ayegbami a Ijebu Ode a jihar Ogun.

“Mamaciyar ta zargeni ne da satar mata waya. A duk lokacin da ta zargeni, sauran ‘yan hayar na goyon bayanta. Suna zagi na tare da min ihu,” jaridar The Punch ta ruwaito yana cewa.

“A ranar juma’a da wajen karfe 5:30 na safe ne naji tana zagina da yarbanci. Ta zargeni da satar mata waya. Kawai sai na yanke hukuncin harar ta da adda. Na sara mata a kai amma sai wasu ‘yan gidan suka nemi kwatarta, suma kuwa sai na bi su da ita.” Ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: