Annobar Lassa ta halaka mutane 8, babban Likita da wani hakimi a jahar Bauchi

Annobar Lassa ta halaka mutane 8, babban Likita da wani hakimi a jahar Bauchi

Annobar zazzabin cutar Lassa ta yi sanadiyyar mutuwar wani babban likita dake aiki a cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya na garin Azare na jahar Bauchi, da wani babban hakimi da kuma wasu mutane 8.

Daily Trust ta ruwaito wata majiya mai karfi daga asibitin koyarwa na jami’ar jahar Bauchi ta bayyana mata cewa wani likita mai suna Mansur Mohammed ya rasu a sanadiyyar zazzabin Lassa a ranar Juma’a, 13 ga watan Maris.

KU KARANTA: Toh fa! Likitan Najeriya ya mutu a sanadiyyar cutar Coronavirus

Majiyar ta bayyana cewa Dakta Mansur tare da wata ma’aikaciyar jinya sun kamu da cutar ne bayan kulawa da wani mara lafiya dake dauke da cutar a FMC Azare, daga nan aka garzaya dasu asibitin koyarwa na ATBU.

“Dukansu biyu sun mutu, kuma a yanzu akwai likitoci guda 5 da aka killacesu sakamakon kamuwa da suka yi da cutar.” Kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Baya ga jami’an kiwon lafiyan da suka mutu, akwai wani mai rike da sarautar gargajiya da shi ma ya rasa ransa a sanadiyyar cutar, shi ne Alhaji Garba Adamu Toro, Katukan Bauchi kuma hakimin Toro.

Sakamakon sake bullar wannan cutar, gwamnan jahar Bauchi, Bala Muhammad ya katse tafiyar da yayi zuwa kasar Jamus, inda ya dawo gida Najeriya don duba hanyoyin shawo kan cutar, kai tsaye ya fara zarcewa ofishin hukumar kula da yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC, dake Abuja.

A cewar gwamnan: “Saboda yaduwar cutar Lassa a Bauchi, da kuma mutuwar hakiminmu tare da jami’an kiwon lafiyan yasa na yanke tafiyar da na yi domin na dawo gida na nemi tallafin gwamnatin tarayya ta hannun shugaban NCDC.”

Daga karshe gwamnan ya bayyana cewa zai hada kai da kungiyoyin addinai da shuwagabannin al’umma domin wayar da kan jama’a game da illolin cutar Lassa tare da hanyoyin kauce ma kamuwa da cutar.

A wani labarin kuma, karamin ministan harkokin kiwon lafiya, Adeleke Mamora ya bayyana cewa an samu wani likita dan Najeriya da ya rasa ransa a sakamakon annobar cutar Coronavirus a kasar Canada.

Minista Mamora ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin da yake bayar da jawabi a kan cutar Coronavirus ga manema labaru inda yace sunan wannan likita dan Najeriya Olumide Okunuga.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel