Buhari ya fasa ciyo bashin naira tiriliyan 8.3 saboda annobar Coronavirus

Buhari ya fasa ciyo bashin naira tiriliyan 8.3 saboda annobar Coronavirus

Gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dakatar da yunkurin da take yi na ciyo bashin dala biliyan 22.7, kimanin naira tiriliyan 8.3 domin gudanar da wasu manyan ayyuka.

Ministar kudi, Zainab Shamsuna Ahmad ce ta bayyana haka a yayin wani taro da hukumar kula da hannun jari ta Najeriya ta shirya inda tace gwamnatinta fasa karbar bashin ne saboda halin da tattalin arzikin duniya ta shiga a yanzu.

KU KARANTA: Toh fa! Likitan Najeriya ya mutu a sanadiyyar cutar Coronavirus

A cewar Shamsuna, koda majalisun dokokin Najeriya sun amince ma gwamnati ta ciyo bashin, a gaskiya ba zasu cigaba da kokarin ciyo kudaden ba, saboda Alkalumman kasuwanci a yanzu sun nuna rashin amfanin ciyo bashin a yanzu.

“Koda majalisa ta amince mana game da ciyo bashin, ba zamu ciyo bashin ba, har sai mun ga cigaban da aka samu a tattalin arzikin kasa.” Inji ta. Haka zalika ta kara da cewa gwamnati na cigaba da kokarin karkatar da akalar tattalin arzikin Najeriya zuwa wasu fannoni, musamman duba faduwar farashin mai da kuma bullar annobar Corona.

Don haka ministan ta ce zasu mayar da hankali wajen kashe kudade a kan manyan ayyukan more rayuwa da zasu fi samar da alfanu ga jama’a, tare da samar da ayyuka ga jama’a tare da saukaka yanayin kasuwanci a Najeriya.

A wani labarin kuma, hukumar bada agajin gaggawa ta kasa, NEMA, ta bayyana cewa jami’anta sun kwashe gawarwakin mutane 15, daga ciki har da na wasu mutane 4 yan gida daya bayan fashewar bututun mai da tukunyar iskar gas a unguwar Abule Ado ta jahar Legas.

Mazauna unguwar sun bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon tarin tukunyoyin iskar gas na kamfani dake jibge a yankin, wadanda suka fashe, har suka shafi bututun mai mallakin wani kamfani mai zaman kansa.

Bugu da kari akwai akalla daliban kwalejin sakandarin mata na Bethlehem guda 50 ne suka samu munana rauni a sakamakon harin, amma an garzaya dasu asibitin rundunar Sojin ruwa dake Ojo Cantonement.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel