A kowace shekara, yan Najeriya na kashe N14bn kan Janareto – Bankin cigaban Afrika

A kowace shekara, yan Najeriya na kashe N14bn kan Janareto – Bankin cigaban Afrika

Diraktan bankin cigaban nahiyar Afrika, shiyar Najeriya, Ebrima Faal, ya laburta cewa yan Najeriya na kasha kimanin bilyan 14 a shekara kan na-urar janareto da man fetur a shekara sakamakon rashin wutan lantarki.

Ebrima Faal ya bayyana hakan ne a taron masu ruwa da tsaki a Abuja inda ya kara da cewa hakan ya taimakawa rashin ingancin wutan lantarki.

Hakazalika, bankin cigaban Afrika AFDB ta bada tallafin $210 million domin inganta wutan lantarki a Najerya.

Tabbatar da hakan, dirakta janar na cibiyar kasuwanci da masana-antun jihar Legas, Muda Yusuf, yace lallai akwai gaskiya cikin maganar AfDB saboda masu kamfanoni na kasha makudan kudi wajen samawa kansu wutan lantarki ta hanyar amfani da Janareto.

Yusuf yace: “Babu yadda za a yi sai kasha wadannan kudaden wajen samar da wutan lantarki muddin ana son masu kamfanoni su cigaba da zama a Najeriya.“

A cewarsa, abin takaici ne a ce bayan shekaru 59 da samun yancin kai, kasa irin Najeriya ta gaza samawa kanta isasshen wutan lantarki.

KU KARANTA Hukumar yaki da rashawar jihar Kano za ta sake sammatar Sanusi Lamido

A kowace shekara, yan Najeriya na kashe N14bn kan Janareto – Bankin cigaban Afrika

A kowace shekara, yan Najeriya na kashe N14bn kan Janareto
Source: Depositphotos

A bangare guda, Majalisar dattijan kasar nan ta fara yunkurin saka dokar daure duk wanda ke siya da siyar da injin samar da wutar lantarki na shekaru 10. Dokar na son hana shigowa da kuma amfani da janareto a kasar nan tare da shawo kan gurbacewar iska.

Dokar haramta amfani da janareton an karanta ta karo na farko ne a zaman majalisa a ranar Laraba. Mataimakin shugaban kwamitin noma da raya karkara, Sanata Muhammed Enagi Bima na jam’iyyar APC ne ya dau nauyin dokar.

Majalisar dattijan Najerriya na yunkurin haramta siya da siyen janareto tare da daurin shekaru 10 ga masu laifin

Majalisar dattijan Najerriya na yunkurin haramta siya da siyen janareto tare da daurin shekaru 10 ga masu laifin.

Da wannan dokar da ake son tabbatarwa, ana bukatar kowa ya daina shigowa da kayyayakin samar da wutar lantarki masu amfani da fetur ko kalanzir a duk fadin kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel